‘Yan Sanda sun cafke wasu Malamai saboda sun yi korafi a kan Shugaban Ma'aikata

‘Yan Sanda sun cafke wasu Malamai saboda sun yi korafi a kan Shugaban Ma'aikata

  • Kwanakin baya wata kungiya ta rubuta takardar korafi a game da Darekta Janar na cibiyar NARICT
  • Ahmad Palladan da Bashir Ibrahim Bomo sun ce Farfesa Tsware Barinas Jeffery ya zarce wa’adinsa
  • Ana zargin a dalilin taba shugaban makarantar ne ‘yan sanda suka kama wadannan malamai

Kaduna - Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna, sun damke wasu malamai a Zaria, saboda korafin da suka rubuta a kan shugaban cibiyar NARICT.

Daily Trust ta tabbatar da cewa an kama wadannan mutane biyu; Dr. Ahmad Aliyu Palladan da Malam Bashir Ibrahim Bomo a ranar Asabar da ta wuce.

Dr. Ahmad Aliyu Palladan da Malam Bashir Ibrahim Bomo sun aika da korafi ne zuwa ga shugaban kasa a karkashin inuwar Concerned Zaria Citizens.

Palladan da Bomo su na koyarwa ne a makarantun koyon aikin malanta na tarayya watau FCE Zaria da FCE Gombe, su na kalubalantar shugaban NARICT.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamnatin El-Rufai ta sanar da ranar da za ta fara daukar malamai 10,000

Malaman su na ikirarin ya kamata Farfesa Tsware Barinas Jeffery ya sauka daga kujerarsa tun da a sabuwar doka, ba zai iya wuce shekara biyar a ofis ba.

A korafin da suka rubuta kwanaki, Ahmad Palladan da Bashir Bomo sun ce wa’adin Darekta Janar din ya cika tun 2021, amma aka kara masa shekara daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan Sanda
Dakarun 'Yan Sanda na kasa Hoto: @Ngpolice
Asali: Facebook

Ko bayan kara masa shekara guda a 2021, ya kamata ya bar kujerar shugaban NARICT, amma har yanzu shi ne ke rike da cibiyar, wanda suka ce ya saba doka.

Takarda ta jawo dauri

A dalilin wannan korafi, jaridar Dateline ta ce ake zargin ‘yan sanda su ka je gidajen malaman makarantar da ke garin Zaria, suka yi gaba da su zuwa garin Kaduna.

A halin yanzu, Legit.ng Hausa ta samu labari malaman su na hannun ‘yan sanda a Gabasawa.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

An dauki sa'o'i 24 shiru

Da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya bukaci a fada masa sunayen wadanda ake zargin an kama, da nufin ya yi bincike a kai.

Har zuwa yanzu babu wani labari, sai dai ma daya daga cikin malaman ya fadawa lauyansa sun shafe sa’o’i 24 a tsare, ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba.

POSN suna kuka

Ku na da labari ‘Yan kungiyar Peter Obi Support Network sun fito suna zargin Gwamna Nasir El-Rufai da bada umarnin hana su dakin taron Arewa House.

Kakakin ‘Yan Peter Obi Support Network wanda aka fi sani da POSN, Kwamred Sani Altukry ya ce babu gaira babu dalili, aka ki ba su damar hayar wajen taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng