Auren manya: Ana babban shiri, dan tsohon shugaban kasa 'Yar Adua zai angwance
- Dan tsohon shugaban kasa, Umaru Musa 'Yar Adua zai angwance nan ba da jimawa ba, ana ta shirye-shirye
- Rahoton da muka samo ya bayyana mambobin kwamitin shirye-shirye na bikin kamar yadda majiyoyi suka tabbatar
- Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua na daga cikin shugabannin Najeriya da suka rasu yayin da suke kan karagar mulki
FCT, Abuja - Abokan marigayi tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa 'Yar' Adua na shirye-shiryen daura auren dan gidan marigayin mai suna Shehu.
A ranar Asabar 23 ga watan Yuli ne Shehu zai angwance a birnin Maiduguri ta jihar Borno, inji rahoton Daily Trust.
Amaryarsa mai suna Yacine diyar Hon. Mohammed Nur Sheriff ce.
A cewar majiyoyi, kwamitin tsare-tsare karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, sun yi taro a ‘yan makonnin da suka gabata a gidan uwargidan tsohon shugaban kasar domin shirye-shiryen auren a Maiduguri.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shehu dan shekara 29, ya samu digirin sa na farko a fannin tattalin arziki daga makarantar kasuwanci ta Schellhammer da ke kasar Spain, sannan ya yi digiri na biyu a fannin hulda da kasashen duniya daga jami’ar Webster da ke kasar Netherlands.
Amaryar, Yacine, mai shekaru 22, ta yi digirin farko a fannin kula da baki daga Jami’ar Surrey da ke Birtaniya.
Mambobin kwamiti
Kwamitin tsare-tsare na karkashin jagorancin Yayale ne tare da tsohon ministan tsaro, Alhaji Lawal Batagarawa a matsayin mataimaki da Birgediya Janar Mustapha Dennis Onoyiveta (rtd), tsohon ADC zuwa Yar’adua a matsayin sakatare.
Hakazalika, akwai kuma kananan kwamitoci guda shida da aka kafa duk dai don shirin wannan biki.
Karamin kwamitin kudi na karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kebbi ne, Sanata Muhammed Adamu Aliero, tare da tsohon shugaban PDP na kasa, Alhaji Adamu Muazu a matsayin mataimakinsa. Dr Tanimu Yakubu Kurfi shine sakatare.
Sauran mambobin babban kwamitin sun hada da Sanata Sanusi Daggash, Dr Aliyu Modibbo, Sanata Garba Yakubu Lado, Alhaji Ikra Aliyu Bilbis, Alhaji Shehu Inuwa Imam, Amb. Habib Baba Habu, Mr Matt Aikhionbare da Dr Salisu Banye.
Akwai kuma Alhaji Mustapha Batsari, Amb. Sani Bala, Amb. Bashir Yuguda, Alhaji Kashim Ibrahim-Imam, Amb. Sani Bala, Alhaji Inuwa Baba, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, Alhaji Abubakar Yar’Adua, Mr Mustapha Yar’Adua da Malam Abubakar Mohammed.
Hakazalika da Malam Bashir Maimaje, Mr Mohammed Adamu, Amb. Haroon Umar, Alhaji Ibrahim Mohammed, Lt Col Abdulaziz Yar’Adua (rtd), Mr Dahiru Dodo, Hajiya Hafsatu Yar’Adua, Malam Isa Mamman Charanchi, Malam Muntari da Alhaji Aminu Maigari.
Akwai kuma rahotannin cewa Uwargidan tsohon shugaban kasa, Mrs Patience Jonathan na daga cikin kirjin bikin da za a yi nan kusa.
Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau
A wani labarin, an tsananta tsaro a duk wasu hanyoyi da za su kai garin Bichi, inda masarautar sarkin Bichi take, Alhaji Nasir Ado Bayero, sakamakon daurin auren diyarsa Zahra, da dan shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tal, Yusuf da za a daura yau a masarautar.
Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha
Daurin auren shine batun da ake magana akai tun watanni da dama da suka gabata a kafafen sada zumuntar zamani kuma cece-kuce iri-iri sun yawaita inda ake cewa biki ne na shugabannin kasa da masu sarauta.
Ana sa ran shugaba Buhari wanda bai dade da dawowa daga wata tafiyar aiki da neman lafiya ba ya halarci daurin auren dan nasa kamar yadda kwamitin tsare-tsare wacce masarautar Bichi ta kafa ta shirya.
Asali: Legit.ng