Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau

Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau

  • A yau ne masarautar Bichi dake jihar Kano za ta amshi manyan baki sakamakon daurin auren dan shugaba Muhammadu Buhari daya tal, Yusuf, da diyar sarkin Bichi
  • Dama an yi watanni jama’a a kafafen sada zumuntar zamani suna ta cece-kuce akan bikin, wanda ake yiwa lakabi da auren shugabannin kasa da na sarakai
  • Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wakilai da suka hada da kusoshin gwamnatin domin halartar bikin auren a masarautar Bichi

Kano - An tsananta tsaro a duk wasu hanyoyi da za su kai garin Bichi, inda masarautar sarkin Bichi take, Alhaji Nasir Ado Bayero, sakamakon daurin auren diyarsa Zahra, da dan shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tal, Yusuf da za a daura yau a masarautar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

Daurin auren shine batun da ake magana akai tun watanni da dama da suka gabata a kafafen sada zumuntar zamani kuma cece-kuce iri-iri sun yawaita inda ake cewa biki ne na shugabannin kasa da masu sarauta.

Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau
Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau. Hoto daga @wraith_studios
Asali: Instagram

Ana sa ran shugaba Buhari wanda bai dade da dawowa daga wata tafiyar aiki da neman lafiya ba ya halarci daurin auren dan nasa kamar yadda kwamitin tsare-tsare wacce masarautar Bichi ta kafa ta shirya.

Ana sa ran jami’an tsaro za su tsananta tsaro tun daga garin Kano har Bichi kusan tafiyar Kilomita 30 don daurin auren da za a yi da misalin karfe 1:30pm a babban masallacin Bichi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Neman auren Gimbiya Zahra Bayero

A watan Yuni, fiye da gwamnoni 7 ne suka isa masarautar Kano wurin yayan mahaifin Zahra, Sarki Aminu Ado Bayero don shirin auren.

Kara karanta wannan

Kayatattun Hotuna da Bidiyoyin Shagalin Kamun Gimbiya Zahra Bayero da Yusuf Buhari

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, bayan ziyarar ne, sarkin mahaifin amaryar ya kafa kwamitin mutane 145 na tsara bikin wanda za a yi ranar Asabar.

Duk da dai kowa ya san Yusuf, amma babu wanda ya san Zahra sai da aka sanya ranar aurensu.

Amaryar mai shekaru 20 tana shekarar karshe a wata jami’a a Amurka wacce ake tunanin a nan suka hadu da Yusuf. Tana karanta tsarin gine-gine. Itace diyar Alhaji Nasir Ado Bayero ta biyu.

Tsatson amarya, Gimbiya Zahra Nasir Bayero

Mahaifiyar Zahra, Farida Imam diyar babban malami ce a Kano, Malam Abubakar Imam (Imamu Galadanci), tsohon darektan Afribank Plc. 'Yar uwar mahaifiyarta tana auren Sarkin musulmi na Sokoto, Muhammadu Sa’ad III.

Sarki ya nuna damuwarsa kan rabuwa da diyarsa da zai yi

A wata tattaunawa da akayi da sarkin Bichi, ya bayyana irin radadin da yake ji na bayar da auren yaransa saboda matukar shakuwar dake tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

A cewarsa, farkon shekarar nan ya bayar da auren yayarta, Daily Trust ta ruwaito.

Inada matukar kusanci da yarana don haka aurar da Zahra babban lamari ne a wurina, amma mun gode Allah.
Yarinya ce karama mai shekaru 20 kuma tana shekarar karshe tana karatu a fannin gine-gine.
Na so Zahra ta tsaya ta kammala karatunta don mu kara yin wasu shekaru a tare amma bamu isa mu canja tsarin Allah ba, ina musu fatan rayuwar aure mai albarka,” a cewarsa.

Mai martaba Nasir Ado Bayero babban dan kasuwa ne wanda yanzu haka shine shugaban kamfanin sadarwa na 9mobile da wasu kamfanoni, ya ce ya yi amfani da fadin manzon Allah (SAW) wanda yace, ‘Idan ka taso da yara mata 3 cikin tarbiyya kuma ka aurar dasu, Allah zai sama maka masauki a Aljannah’.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel