Yajin aiki: Ma'aikatan jiragen sama zasu rufe filayen jirage don taya ASUU nuna fushi
- Kungiyar ma'aikatan jiragen sama sun nuna fushi kan yadda gwamnatin Buhari ta gaza shawo kan matsalar yajin aikin ASUU
- ASUU ta shafe akalla watanni hudu tana yaji kan wasu bukatu da ta bijiro dasu amma gwamnati ta nuna ba lallai a iya cika su ba
- An sha samun lokuta da dama da kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aiki duk dai saboda rashin samun abin da take so daga gwamnati
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta shiga yi ko kuma za su rufe bangaren sufurin jiragen sama tare da hada kai da malaman jami’o’in.
A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrasaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba, rahoton Leadership.
ANAP ta lura cewa ci gaba da zama a gida da daliban manyan makarantu ke yi na kara haifar da munanan dabi’u a kasar nan yayin da dalibai ke yin wasu abubuwa marasa kyau da ke iya lalata makomarsu.
ANAP ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aikin na hadin gwiwa ta hanyar rufe bangaren sufurin jiragen sama idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa na biyan bukatun ASUU ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar ta lura cewa yajin aikin na sama da watanni hudu ya kawo cikas ga harkar ilimi, kana ya zama abin dariya a idon duniya.
Saidu ya kara da cewa:
“Yaranmu na bata shekaru takwas don karanta kwasa-kwasan shekaru hudu tsabaragen almubazzaranci. Ba za mu iya ci gaba da haka ba."
Ya kuma yi nuni da cewa yawancin ‘ya’yan ‘yan siyasar Najeriya suna karatu ne a kasashen waje yayin da harkar ilimi a Najeriya ke neman tabarbarewa.
Wata sabuwa: Babu wata yarjejeniya tsakanimu da ASUU, inji gwamnatin Buhari
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce babu wata yarjejeniya ta hadin gwiwa (CBA) tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’i wao ASUU da ke jiran sa hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Olajide Oshundun, ya fitar ranar Laraba, inji Daily Trust.
A cewar wani yanki na sanarwar da ke rusa bayanin yarjejejiyar hadin gwiwar maslaha tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU, ma'aikatar kwadagon ta ce:
Asali: Legit.ng