Kungiyar CAN ta yi korafi akan yawan sace-sacen Mambobinta a Najeriya

Kungiyar CAN ta yi korafi akan yawan sace-sacen Mambobinta a Najeriya

  • Kungiyar Kristocin Najeriya CAN, ta bayyana bakicin ciki da damuwa akan yadda sace Fastocin da mabiyan su ya zama ruwan dare a jihar Kaduna
  • Rabaran Joseph Hayab ya ce adadin limaman Cocoin Katolika da aka sace a cikin shekaru uku ya kai goma sha takwas 18
  • Yan Bindiga sun awon gaba da limaman Cocin Katolika biyu a yammacin ranar juma'a a jihar Kaduna

Jihar Kaduna - Kungiyar Kristocin Najeriya CAN, ta bayyana bakicin ciki da damuwa akan yadda sace Fastocin da mabiyan su ya zama ruwan dare a jihar Kaduna da wasu sassar Najeriya. Rahoton BBC

Jagoran kungiyar CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya bayyana haka da yake tattaunawa da waikilan BBC, Inda ya ce :

“Sace- sacen limaman cocin Katolika ya zaman ruwan dare mussaman a jihar Kaduna da kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kara yin garkuwa da limaman cocin Katolika a jihar Kaduna

Jospeh
Kungiyar CAN ta yi korafi akan yawan sace-sacen Mambobinta a Najeriya FOTO THE CABLE
Asali: UGC
”A tunaninmu yakamata a ce an riga na shawo kan wannan matsalar satar mutane amma har yanzu yi a ke.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

”A yanzu haka a jihar Kaduna an saci limaman cocin Katolika kusan goma sha takwas 18 a cikin shekaru uku da suka gabata.”
“Kuma an saci mabiya wanda ba zai iya fadin adadinsu ba, don ina ganin idan aka hada da yaran makaranta da sauran Kiristocin da aka sace a kauyuka adadinsu zai iya kai wa dubbai.

Legit.NG ta rawaito yadda yan bindiga suka yi garkuwa da limaman cocin Katolika guda biyu, Reverend Father John Cheitnum da Reverend Father Donatus Cleopas a yammacin ranar Juma’a 16ga watan Yuni a karamar hukumar Jere (LGA) ta jihar.

'Yan Bindiga Sun kara Sace Limaman cocin Katolika Biyu A Kaduna

A wani labari makamacin wannan, Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu limaman cocin Katolika guda biyu a jihar Kaduna, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da limaman cocin guda biyu, Reverend Father John Cheitnum da Reverend Father Donatus Cleopas a yammacin ranar Juma’a a karamar hukumar Jere (LGA) ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa