Zamfara: Hatsabibin Dan Bindiga Da Ya Dade Yana Addabar Mutane Zai Zama Sarki
- Masarautar Yandoton Daji a za ta nada hatsabibin shugaban yan bindiga, Adamu Aleru sarautar sarkin Fulani a Yandoton Daji
- Majiya daga garin ta ce dattawan garin sun yanke shawarar yin sulhun da yan bindigan ne domin sun cire tsammanin gwamnati za ta iya yakarsu yayin da suke addabarsu a kullum
- Sarautar da za a yi wa Aleru, ana fatan za ta saka ya janyo hankulan sauran manyan shugabannin yan bindiga na yankin su rungumi sulhu da al'umma
Zamfara - Idan har gwamnatin Jihar Zamfara bata dauki matakin hana wa ba, an kammala shiri don nada hatsabibin dan bindiga, Adamu Aleru, a matsayin Sarkin Fulani a masarautar Yandoton Daji a ranar Asabar.
Majiyoyi daga yankin wadanda suka nemi a boye sunansu saboda tsaro, sun shaidawa Premium Times cewa an yanke shawarar nada dan ta'addan sarauta ne don samun dawamammen zaman lafiya a masarautun Tsafe da Yandoton Daji da wasu yankunan jihohin Zamfara da Katsina, da Aleru da makarrabansa suka saba kai hari.
Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yandoton Daji na cikin sabbin masarautu biyu da gwamnatin Jihar Zamfara ta kirkira a watan Mayu. An kirkire ta ne daga masarautar Tsafe. Sarkin Yandoton shine Aliyu Marafa.
An yanke shawarar yi wa Aleru sarauta ne bayan tattaunawa da dattawan masarautar suka yi da shugaban yan ta'addan.
Premium Times ta rahoto a watan Maris cewa yayin hirar, dattawan masarautan sunyi kira ga Aleru ya dena kaiwa garuruwansu hari.
"Aleru ya tara kudi masu yawa da shanu kuma ya san cewa idan wannan (yakin da sojoji) ya cigaba, daga karshe zai rasa shanunsa da dukiyarsa. A matsayin jagorar mafi yawan yan bindiga a Yankuzo da Munhaye, da ma Tsafe, yana ganin gara ya yi sulhu," wani majiya, mazaunin yankin ya ce.
Wani majiya, ma'aikacin gwamnati a garin Tsafe, ya ce an yanke shawarar yi wa Aleru nadin sarauta ne don nuna godiya bisa zaman lafiya da aka fara samu a yankunan.
Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha
"An yi taro a Yandoto makonni biyu da suka wuce kuma wadanda suka hallarci taron sun ga yadda Adamu Aleru ke aiki don ganin nasarar sulhun. Bai roki a bashi sarauta ba amma masarautar na ganin idan an bashi, hakan zai daure shi," majiyar ta ce a ranar Alhamis.
Ya kara da cewa yan bindigan ya yi sallar Idi tare da musulmi a Tsafe a ranar Asabar, abin da ake yi wa kallon wani alama ne da ke nuna ya amince da sulhun.
"Na tafi Idin kuma na ga lokacin da shi (Aleru) ya zo da yaransa da iyalansa. Babu wanda ke rike da bindiga," in ji ma'aikacin gwamnatin.
Ya kuma kare yunkurin da ake yi na bawa Aleru sarauta
"Yaushe ne ranar karshe da muka kira don fada muku an kai hari a yankin Tsafe? Na san wasu ba za su yi farin ciki da wannan ba amma gwamnati za ta iya yaki da yan bindigan?".
Peter Obi: : Sowore Ya Bayyana Tsaffin Shugabanin Najeriya 3 Da Jigon Arewa Da Ke Goyon Bayan Jam'iyyar Labour Party
Ya kara da cewa ana fatan Aleru zai taho tare da sauran hatsabiban yan bindiga kamar Ali Zakwai, Bello Turji, Danboko, Sanata, Isuhu Yelo, Damina, da Mai Shamuwa.
Ba a samu ji ta bakin yan sanda ko gwamnati ba
Zailani Bappa, kakakin gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da kakakin yan sanda, Mohammed Shehu, ba su amsa kira da sakon tes da aka aike musu kan batun ba.
Amma, Wakilin Masarautan Yandoton Daji, Magaji Lawal ya shaidawa Premium Times cewa masarautar za ta bawa Aleru sarauta ne a kokarinta na karfafa sulhu da ake yi.
"Eh, zan iya tabbatarwa za a nadi shi sarauta a yau. Muna hakan ne don karfafa yarjejeniyar zaman lafiya saboda ana kashe mutanen mu ko sace su a kullum," ya shaidawa Premium Times a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng