Fyade : Kotu ta yankewa Baba Ijesha hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari

Fyade : Kotu ta yankewa Baba Ijesha hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari

  • Kotu ta yanke wa Olanrewaju James, wanda aka fi sani da Baba Ijesha hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari bisa laifin lalata da karamar yarinya
  • Baba Ijesha fitaccen jarumin fina-finan Nollywood na Yarbawa ne wanda aka fi sanin shi da wasan barkwanci
  • Baba Ijesha ya samun lambar yabo a wasan barkwanci na Najeriya kuma ya taka rawa sosai a shahararrun finan finan Yarbawa

Jihar Legas - Kotun da ke zamanta a unguwar Ikeja ta jihar Legas ta yankewa jarumin fina-finan Nollywood, Olanrewaju James, wanda aka fi sani da Baba Ijesha hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari bisa samunsa da laifin yin lalata da karamar yarinya ‘yar shekara 14. Rahoton Channel Television

Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo, a hukuncin da ya dauki tsawon sa’o’i biyu, ya kuma kama Baba Ijesha da laifika hudu daga cikin laifuka shida da ake tuhumarsa da su.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Babu wata yarjejeniya tsakanimu da ASUU, inji gwamnatin Buhari

iJESHA
Fyade : Kotu ta yankewa Baba Ijesha hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari FOTO Legit.NG
Asali: Instagram

An yankewa Baba Ijesha hukuncin akan laifin cin zarafin karamar yarinya da kuma nufin yin lalata da ita.

Sai dai alkalin ya wanke shi daga laifi biyu daga cikin laifuka shida, wadanda suka hada da cin zarafi ta hanyar shafar jinkita da kuma yunkurin saduwa da ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun ta ce masu gabatar da kara ba za su iya tabbatar da wadannan laifukan ba.

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

A wani labari, Plateau - Tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Victor Dimka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2023.

Dimka, wanda ya kasance tsohon kwanturolan hukumar kwastam a wata hira da manema labarai a garin Jos, ya ce Tinubu dan siyasa ne da ya yarda da hadin kai da ci gaban Najeriya a matsayin kasa daya, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU

Asali: Legit.ng

Online view pixel