Limamin JIBWIS, Sheikh Umar Maigona, ya rasu a kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajji
- Allah ya yiwa shahararren malamin musulunci kuma mamba na hukumar jin dadin alhazai na jihar Gombe, Sheikh Abdulrahman Umar Maigona, rasuwa
- Maigona wanda ya kasance limamin masallacin JIBWIS da ke No. 8, Gombe, ya kwanta dama ne a kasar Saudiyya a ranar Alhamis
- Marigayin ya dan yin fama da yar rashin lafiya inda daga bisani ya cika dauke da kalmar shahada a bakinsa
Saudiyya - Shahararren malamin musulunci kuma mamba na hukumar jin dadin alhazai na jihar Gombe, Sheikh Abdulrahman Umar Maigona, ya rasu a Makkah, kasar Saudiyya.
Maigona ya kwanta dama ne bayan kammala aikin hajjin 2022.
Marigayin wanda ya kasance limamin masallacin JIBWIS da ke No. 8, Gombe, ya koma ga Allah a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli, masaukin Namma Muwada, bayan yar gajeriyar rashin lafiya, Muslim News Nigeria ta rahoto.
Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya
Shugaban tawagar kiwon lafiya na hukumar aikin hajji ta kasa, Dr Usman Shu’aibu Galadima, wanda ya tabbatar da ci gaban ya ce an shigo da Maigona da misalin karfe 1:00 na rana kuma nan take aka shiga kula da shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, yanayinsa ya yi tsanani kuma a kokarin daidaita shi sai ya amsa kiran mahaliccinsa.
Galadima ya ce marigayin ya ziyarci cibiyar lafiyar sau daya kuma an yi masa maganin Wani rashin lafiya.
A cewar wani shaida, malamin ya yi kalmar shahada kafin ransa ya fita.
An dauki gawar Sheikh Maigona zuwa masallacin harami domin yi masa jana’iza.
Har zuwa mutuwarsa, marigayin ya kasance lakcara a sashin koyon addinin islama na jami’ar jihar Gombe kuma babban limamin masallacin Izala.
Marigayin mai shekaru 48 ya kasance na hannun damar ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Maigona shine mahajacci na uku da ya mutu a yayin aikin hajjin 2022.
Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi a jihar Nasarawa ta mutu a ranar 29 ga watan Yuli, bayan yar gajeriyar rashin lafiya kuma an binne ya a Makkah, yayin da Hajiya Hasiya Aminu daga Zaria, jihar Kaduna ta rasu a ranar Arafat, 8 ga watan Yuli.
Allah ya yiwa mai kula da masallacin Manzon Allah, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa
A wani labarin, mun ji cewa Allah ya yiwa daya daga cikin wadanda suka dade suna yi wa Masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi hidima, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa.
Marigayin shine kuma ke kula da dakin da kabarin Annabi Muhammad yake.
Muhammad al-Afari ya rasu ne a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, kamar yadda shafin Haramain Sharifain @hsharifain ya wallafa a Twitter.
Asali: Legit.ng