Sunaye: Manyan kwamandojin yan ta’adda 6 sun mika wuya yayin da sojoji suka kashe mayaka 42

Sunaye: Manyan kwamandojin yan ta’adda 6 sun mika wuya yayin da sojoji suka kashe mayaka 42

  • Manyan kwamandojin kungiyar ta'addanci na Boko Haram su shida sun mika wuya a jihar Borno
  • Kwamandojin sune Mallam Mala Hassan (WALI), Ali Madagali (MUNZUR), Musa Bashir (CIF ANUR), Buba Dahiru (MUNZUR), Jafar Hamma (KAID) da Abbali NAKIB Polisawa
  • Dakarun sojojin Operation Hadin kai sun kuma kashe mayakan kungiyar ta'addancin su 42 cikin makonni biyu

Borno - Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa manyan kwamandojin yan ta’adda shida sun mika wuya a jihar Borno yayin da dakarun soji suka kashe mayaka 42 a yankin arewa maso gabas cikin makonni biyu.

Daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko, ne ya bayyana hakan a yayin jawabinsa na mako-mako kan ayyukan rundunar sojojin Najeriya daga 30 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin 2022, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar cin mutuncin Buhari a Kogi

Sojoji
Sunaye: Manyan kwamandojin yan ta’adda 6 sun mika wuya yayin da sojoji suka kashe mayaka 42 Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ya ce dakarun Operation HADIN KAI na ci gaba da kai yaki da Boko Haram da ISWAP har zuwa mabuyarsu inda a ranar 13 ga watan Yulin 2022, manyan kwamandojin yan ta’adda suka mika wuya ga rundunar a Gwoza.

"Yana da kyau a lura cewa tun bayan da 'yan ta'adda suke mika wuya ga sojojinmu ba a taba garin irin manyan kwamandojin da suka mika wuya a wannan lokaci ba daga cikinsu akwai WALI (Gwamna) da KAID (Kwamanda mai tauraro 3)" in ji shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya lissafa yan ta’addan da suka mika wuya kamar haka:

  1. Mallam Mala Hassan (WALI)
  2. Ali Madagali (MUNZUR)
  3. Musa Bashir (CIF ANUR)
  4. Buba Dahiru (MUNZUR)
  5. Jafar Hamma (KAID)
  6. Abbali NAKIB Polisawa.

Ya kara da cewar kimanin yan ta’addan Boko Haram 3,858 da iyalansu ma sun mika wuya tsakanin 1 da 14 ga watan Yuli, wadanda suka hada da maza 505, mata 1,042 da yara 2,311.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya shawo kan Gwamnonin APC a kan zaben Shettima da Tinubu ya yi

Kakakin rundunar tsaron ya kuma bayyana cewa dakarun sojojin sun kuma kama masu kaiwa yan ta’adda kayayyaki da dama tare da kayayyaki iri-iri a garuruwa daban-daban cikinsu harda wasu mata biyu, Hauwa Gambo da Khadija Dirsa, rahoton PM News.

A wani lamari makamancin wannan, ya ce dakarun sojin sama na Operation HADIN KAI a ranar 11 ga watan Yuli sun aiwatar da wani aiki a Tumbum Jaki da Tumbum Murhu kusa da tafkin Chadi da ke jihar Borno sannan suka kashe mayakan Boko Haram da dama tare da lalata mabuyarsu.

Dakarun soji sun kashe kasurguman masu garkuwa da mutane biyu, sun ceto matafiya 9

A wani labarin kuma, dakarun Operation Safe Haven sun kashe wasu kasurguman masu garkuwa da mutane biyu sannan sun kama masu fashi da makami biyu tare da ceto matafiya tara a yankin arewacin kasar.

Daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

Ya yi bayanin cewa sun samu nasara a ayyukan da suka gudanar tare da jami’an yan sanda a tsakanin Alhamis da Asabar na makon da ya gabata a kokarinsu na ganin an yi bikin sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng