Bayan Kama Dan Boko Haram a Nasarawa, Yan Sanda Sun Sake Kamo Wani Cikin Fursunoni Da Ya Tsere Daga Kuje
- Yan sanda sunyi nasarar kama wani fursuna daga cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin Kuje bayan harin yan bindiga
- Kakakin yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a ranar Laraba
- Oyeyemi ya ce wanda aka kama din, Yakubu AbdulMumuni, tunda farko an same shi ne da laifin hadin baki da hannu a kisa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Ogun - Yan sandan Jihar Ogun sun kama wani fursuna dan shekara 28 da ya tsere daga gidan yarin Kuje mai suna Yakubu AbdulMumuni.
An kama wanda ake zargin ne a Santa-Ota, a karamar hukumar Ado/Ota na jihar kamar yadda The Punch ta rahoto.
Kakakin rundunar yan sandan Jihar Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Oyeyemi ya ce yan sanda ne suka yi nasarar kama AbdulMumuni wanda tunda farko aka yi wa dauri saboda laifin hadin baki da kisan kai a Jihar Kogi ne aka kuma tura shi gidan yarin Kuje.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Oyeyemi ya ce, "An kama wanda ya tsere din, Yakubu AbdulMumuni, dan shekara 28 bayan yan sandan Sango Ota divisional hedkwatars sun samu bayanin an hange shi a wani wuri a yankin.
"Bayan samun bayan, DPO na Sango-Ota Division, SP Saleh Dahiru, cikin gaggawa ya tashi tawagarsa suka tafi unguwar suka kamo wanda ake zargin.
"Ya fada wa yan sanda cewa ya tsere daga gidan gyaran hali na Kuje a ranar 5 ga watan Yulin 2022, lokacin da yan bindiga suka kai hari.
"Ya kara da cewa babban kotun jihar Kogi ta yanke masa hukunci saboda laifin hadin baki da hannu a kisa kuma aka tura shi gidan gyaran hali na Kuje."
Kakakin yan sandan, amma, ya ce kwamishinan yan sandan, Lanre Bankole, ya umurci sashin binciken manyan laifuka na CID ta tabbatar an mayar da mai laifin zuwa gidan yarin nan take.
Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sunyi Nasarar Cafke Daya Cikin Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Kuje
Yan Bindiga Sun Kashe Dan Uwan Tsohon Gwamna Adamu Mu'azu, Sun Kuma Sace Iyalansa
A wani rahoton, kun ji cewa an bindige wani Mu'azu Danladi, dan shekara 25, dan uwan tsohon gwamna Ahmad Adamu Mu'azu a kauyen Boto na karamar hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi.
An kashe Danladi ne a lokacin da yan bindigan suka kutsa gidan iyalan Mu'azu a safiyar ranar Laraba.
An sace mutane uku yayin harin da ya bawa mutanen kauyen mamaki.
Asali: Legit.ng