Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa dan majalisa, Olusegun Popoola, rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa dan majalisa, Olusegun Popoola, rasuwa

  • Majalisar dokokin jihar Oyo ta rasa daya daga cikin ‘ya’yanta, Ademola Olusegun Popoola, a safiyar Laraba, 13 ga watan Yuli
  • Marigayi Popoola ne dan majalisar da ke wakiltan mazabar Ibadan ta kudu maso gabas karkashin inuwar jam’iyyar PDP
  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya tabbatar da lamarin inda ya nuna kaduwa da bakin cikinsa kan haka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Allah ya yiwa dan majalisar dokokin jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola, rasuwa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Popoola ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, yana da shekaru 46 a duniya.

Dan majalisar shine ke wakiltan mazabar Ibadan ta kudu maso gabas a majalisar dokokin jihar.

Olusegun Popoola
Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa dan majalisa, Olusegun Popoola, rasuwa Hoto: Pulse Nigeria
Asali: UGC

An tattaro cewa ya rasu ne a asibitin UCH da ke garin Ibadan, babbar birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC

An zabi dan majalisar a 2019 don wakiltan mazabar karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

An kuma tattaro cewa ya rasu ne bayan ya yi fama da cutar koda.

Hon. Popoola ya kasance shugaban kwamitin majalisar kan harkokin karamar hukuma da sarauta.

Mai ba kakakin majalisar jihar, Adebo Ogundoyin, shawara kan harkokin labarai, Oyekunle Oyetunji ya tabbatar da labarin mutuwar dan majalisar a yau Laraba.

Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa da yake tabbatar da lamarin, gwamnan jihar, Seyi Makinde, ya nuna kaduwa sosai kan mutuwar dan majalisar.

Ya bayyana mutuwar dan majalisar a matsayin abun bakin ciki, radadi da kuma babban rashi ga jihar, sannan ya mika ta’aziyya ga PDP.

Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

A wani labari na daban, kungiyar matasan APC a arewa ta jinjinawa dan takarar shugaban kasa na APC da manyan jiga-jigan jam’iyyar kan zabar Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai daga tutar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima

Shugaban kungiyar Hon. Suleiman Liba ya bayyana cewa ba za su yi bacci ba har sai sun ga Tinubu da Shettima sun yi nasara a babban zaben mai zuwa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng