'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyan N4.3bn na fansar Fasinjojin jirgin ƙasa

'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyan N4.3bn na fansar Fasinjojin jirgin ƙasa

  • Yan ta'addan da suka farmaki jirgin kasan Kaduna-Abuja sun nemi a biya miliyan N100m kan kowane mutum ɗaya
  • Bayan kubutar mutum 7 ranar Asabar, shugaban iyalan waɗan da aka sace, Abdulfatai Jimoh, ya ce ya zama saura Fasinjoji 43 hannun su
  • Tukur Mamu, ya ce gwamnatin tarayya ta san bukatun yan ta'addan kuma ya yaba wa gwamnan jihar Ƴobe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - 'Yan ta'adda sun buƙaci a tara musu miliyan N100m kan duk mutum daya daga cikin fashinjojin jirgin ƙasan Kaduna 43, waɗan da ke tsare a hannun su har yau, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sun aike da sakon wannan buƙatar ne ga iyalan mutanen a makon da ya shuɗe. Wannan na zuwa ne kwana biyar bayan waɗan da suka kitsa sace Fasinjojin sun tsere daga gidan Yarin Kuje a harin yan ta'adda ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shagalin Sallah, 'Yan bindiga sun kai mummunan hari kauyukan jihar Zamfara sun kashe mutane

Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki nauyin kai harin a wani Bidiyo da ta saki awanni 24 bayan faruwar lamarin. Maharan sun kwance mayaƙan Boko Haram sama da 300 da wasu Fursunoni da suke tsare.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i.
'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyan N4.3bn na fansar Fasinjojin jirgin ƙasa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta tura bayanan kwamandojin Boko Haram 64 a ma'ajiyar bayanan yan sandan ƙasa da ƙasa, waɗan da suka gudu daga wurin da ake tsare da su a harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar 28 ga watan Maris, 2022, yan bindigan suka farmaki jirgin ƙasa da ke aiki tsakanin Kaduna-Abuja, inda suka kashe mutum 8 kuma suka yi awon gaba da wasu 61.

Abubuwan da suka nema tun bayan sace Fasinjojin

Daga cikin sharuɗdan da suka gindaya, yan ta'addan sun nemi FG ta saki kwamandojin su guda 15 dake tsare, 'ya'yan su da ke hannun sojoji da kuma wasu maƙudan kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Asiri ya Tonu: An kama manyan 'yan sanda biyu sun yi waya da yan ta'adda bayan harin gidan Yarin Kuje

Ranar 12 ga watan Yuni, maharan suka sako mutum 11 bayan shafe kwanaki 75 yayin da wasu mutum Bakwai suka shaƙi iskar yanci ranar Asabar da ta wuce.

Mutanen sun kubuta ne ta hanyar taimakon ɗan jaridan nan na jihar Kaduna, Mallam Tukur Mamu, wanda ke shiga tsakani wajen tattaunawa da yan ta'addan.

Da yake karin haske kan halin da ake ciki ranar Lahadi, wani mamba a iyalan ɗaya daga cikin waɗan da aka sace, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya ce 'yan ta'adda sun nemi kowane gida su biya 100m idan suna son kubutar da ɗan uwan su.

Majiyar ta ƙara da bayyana cewa mutum Bakwai da suka kubuta ranar Asabar sai da iyalan su suka biya makudan kuɗin da ba'a bayyana ba.

Ya ce:

"Kuɗi ne suka jinkirta kubutar da sauran fasinjojin. Yanzun masu garkuwan sun buƙaci fansa, mun ji labarin rukunin baya-bayan nan sun biya kuɗi, sun neme mu game da biyan kuɗin fansa."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

"Halin da ake ciki yanzun idan kana da kuɗi za'a sako ɗan uwanka, sun yanke miliyan N100m, abun da takaici."

Wani mamban iyali daban ya shaida wa wakilin jaridar cewa an gaya musu yan ta'addan ba su sha'awar cigaba da tattaunawa da FG, inda aka ce suna buƙatar miliyan N100m kan fasinjojin.

"Har yanzun ba'a saki ɗan uwana ba, duk wanda suka fito sun biya Miliyan N100m, bani da waɗan nan kuɗin. Sun faɗa mana sun kyale FG. Samun miliyan N100m ba karamin abu bane, da yawan mu bamu da su."

Shin dagaske ne yan ta'addan na neman Miliyan N100m?

Da aka tambaye shi ko gaskiya ne yan ta'addan sun nemi kowane iyali su haɗa N100m, mai shiga tsakani, Tukur Mamu, ya ce gwamnati tasan komai domin ya tura duk abinda suka gaya masa ga FG.

Mamu ya ce:

"Na tura jerin ga gwamnati kuma maganar gaskiya ba abinda ta yi, sakamakon haka ne suka yi barazanar kai hari gidan Yarin Kuje kuma suka yi nasarar kubutar da gomman yan ta'adda maimakon 10 da suka nema."

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan kai wa Ayarin Buhari hari, Jirgin yaƙin NAF ya yi wa yan bindiga ruwan bama-bamai, rayuka sun salwanta

"Ina ganin gwamnati ya kamata ta yi bayani dalla-dalla saboda na sanar mata da komai."

Mamu ya kuma yaba wa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, kan abin da ya kira rawar bayan fage da ya taka wajen kubutar da waɗan nan mutum Bakwai.

Shin hukumomin tsaro sun san da kuɗin fansar?

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya, Peter Afunanya, ya ƙi yarda ya yi tsokaci kan bukatun yan ta'adda yayin da aka tuntuɓe shi ta wayar salula.

A ɗaya ɓangaren kuma, kakakin hukumar yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce ba su da masaniya kan tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.

Shugaban iyalan Fasinjojin da aka sace, Abdulfatai Jimoh, ya ce bayan kubutar mutum Bakwai ranar Asabar, ya zama saura mutum 43 a hannun yan ta'addan.

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa Buhari ya ce ba zai huta ba har sai ya samar wa 'yan Najeriya sassaucin rayuwa da zaman lafiya

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hadimin Sheikh Ahmad Gumi ya fallasa sunan waɗan da suka kai kazamin hari gidan Yarin Kuje

Buhari , ya sake tabbatar wa yan Najeriya cewa ba zai huta ba har sai sun samu nutsuwa daga gare shi duba da kalubalen tsaro da tsadar rayuwa da suka dabaibaye ƙasar nan.

Yayin taya Musulmai murnar zuwan Sallah, Buhari ya ce da kowa na koyi da koyarwan addini da duk matsalolin nan sun zama tarihi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262