Ana shagalin Sallah, 'Yan bindiga sun kashe dandazon mutane a jihar Zamfara

Ana shagalin Sallah, 'Yan bindiga sun kashe dandazon mutane a jihar Zamfara

  • Yayin da al-ummar Musulmai ke cigaba da shagalin babbar Sallah, wasu miyagun yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Zamfara
  • Mazauna ƙauyukan Kango da Ɗangulbi sun ce maharan sun kashe mutum 18 a harin na safiyar Lahadi wato washegarin Sallah
  • Wani ɗan asalin kauyen Ɗangulbi, Sama'ila, ya ce da yawan mutanen da suka tsere yayin harin ba su koma gida ba

Zamfara - Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukan su ranar Lahadi da safe bayan wasu 'yan bindiga da ke bayan kasurgumin ɗan bindigan nan, Damina, sun farmaki ƙauyukan Kango da Ɗangulbi, ƙaramar hukumar Maru a Zamfara.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mazauna ƙauyukan sun tabbatar da haka, inda suka ce da yawan mutanen da suka tsere yayin harin ba su koma ba har yanzu.

Ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara na ɗaya daga cikin yankunan da ayyukan ta'addancin yan bindiga ya fi muni.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya dakatar ayarin motocinsa, ya taimaka wa wasu mutane da suka yi haɗari

Yan bindiga sun kai hari Zamfara.
Ana shagalin Sallah, 'Yan bindiga sun kashe dandazon mutane a jihar Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Tuni dai aka yi wa gawarwakin mutum 18 da suka rasu Jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada, inji wani shugaban ƙauye, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mazaunin cikin garin Maru, Shehu Ismaila, ya ce an kashe bayin Allah 13 a ƙauyen Dangulbi yayin da wasu mutum 5 suka ce ga garin ku nan a ƙauyen Kango.

Sama'ila wanda asalinsa ɗan ƙauyen Ɗangulbi ne ya ce maharan sun kai hari Kango ne da farko kafin daga bisani su zarce ƙauyen Ɗangulbi, inda suka kashe manoman da ke aiki a gonakin su.

Mutumin ya ce:

"An kashe mutum 6 a wajen gari yayin da sauran Bakwai ɗin suka rasa rayuwarsu a cikin gari. Waɗan da aka kashe sun yi sammako ne domin yin wasu ayyuka a gonakin su kafin su dawo gida su cigaba da shagulgulan Sallah."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

Shugaban yan bindiga ya nemi miliyan biyu

Shehu Sama'ila ya kara gaya wa jaridar cewa ƙasurgumin ɗan bindigan, wanda ake kira da Damina ya nemi miliyan biyu daga ƙauyen Ɗangulbi a matsayin harajin kariya, sai dai mutane sun gaza haɗa kudin saboda halin da ake ciki.

Haka zalika, wani shugaban ƙauye ya ce sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna tare da Damina kuma ba su tsammani zai farmaki ƙauyen ba, BBC Hausa ta ruwaito.

Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda na Zamfara, Mohammed Shehu, bai ɗaga kiran waya ba kuma be dawo da amsar sakonnin da aka tura masa ba game da harin.

A wani labarin kuma Gwamnan Arewa ya dakatar ayarin motocinsa, ya taimaka wa wasu mutane da suka yi haɗari

Yayin da yake kan hanyar komawa gidan gwamnati daga Abuja , Gwamna Neja ya tsaya taimaka wa wasu motoci da suka yi haɗari a Paiko.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan kai wa Ayarin Buhari hari, Jirgin yaƙin NAF ya yi wa yan bindiga ruwan bama-bamai, rayuka sun salwanta

Gwamna Abubakar Sani Bello, ya jajantawa mutanen da ke cikin motocin tare da ɗaukar nauyin yi wa masu rauni magani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel