Alhazan Najeriya sunyi korafi akan yadda ake nuna musu Banbanci a Saudiya

Alhazan Najeriya sunyi korafi akan yadda ake nuna musu Banbanci a Saudiya

  • Alhazan Najeriya sunyi korafi akan yadda aka nuna musu bambamci a kasar saudiyya a lokacin aikin Hajji
  • An samar wa Mahajjatan wasu kasashe shimfidar kwanciya a filin muzdalifa amma am ba yan Najeriya kwali su kwanta
  • shugaban likitocin Najeriya a Saudiyya ya ce adadin mahajjatan Najeriya da suka mutu a kasar sun kai tara

Saudiyya - Wasu Mahajjatan Najeriya sunyi korafi akan yadda hukumar kasar Saudiyya ta nuna musu bambanci a zama na Muzdalifa a lokacin aikin Hajjin bana. Rahoton BBC HAUSA

Cikin alhazawan da suka zanta da masu rahoton BBC sun ce akwai bambancin tsakanin Abubwan da hukumar kasar ta tanadar wa mahajjatan Najeriya da wadanda ba yan Najeriya ba.

Abubakar Baban Gwale, da yake wa masu rahoton BBC jawabi ya ce “zaka ga an baiwa mutanen wasu kasashe shimfidar kwanciya a filin Muzdalifa amma mu(Najeriya) babu shimfida sai dai aka nemo kwalaye aka bamu a matsayin shimfida mu kwanta akai.

Kara karanta wannan

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

hajji
Alhazan Najeriya sunyi korafi akan yadda ake nuna musu Babanci a Saudiya : FOTO Legit.Ng

Da ma dai Mahajjatan Najeriya sun yi korafi akan yadda hukumomi suka gaza tanadar musu muhimman abubuwan da suke bukata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun yi zargin karancin abinci da kuma masu kula da lafiyarsu a Saudiyya.

A makon da ya gabata ne Alhazai uku daga jihar Kano, biyu daga jihar Katsina, daya daga jihar Sokoto da kuma daya daga jihar Nasarawa suka ruga mu gidan gaskiya wanda yanzu haka adadin mahajjatan Najeriya da suka mutu ya kai tara

Dr. Ibrahim Kana, Shugaban tawagar likitoci na hukumar kula da mahajjatan Najeriya (NAHCON), ne ya tabbatar da hakan.

Ana shagalin Sallah, 'Yan bindiga sun kashe dandazon mutane a jihar Zamfara

A wani labari - Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukan su ranar Lahadi da safe bayan wasu 'yan bindiga da ke bayan kasurgumin ɗan bindigan nan, Damina, sun farmaki ƙauyukan Kango da Ɗangulbi, ƙaramar hukumar Maru a Zamfara.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mazauna ƙauyukan sun tabbatar da haka, inda suka ce da yawan mutanen da suka tsere yayin harin ba su koma ba har yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa