Da dumi-dumi: Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a Daura
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu da gwamnan jihar Katsina
- Tinubu dai ya isa Daura da ke jihar Kastina a yau Lahadi, 10 ga watan Yuli, domin kaiwa Buhari gaisuwar sallah
- Nan take kuma sai manyan jiga-jigan na jam'iyyar mai mulki a kasar suka shiga cikin wata ganawa ta sirri
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Katsina - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya isa garin Daura da ke jihar Katsina, jaridar Leadership ta rahoto.
Da isarsa Katsina, Tinubu ya samu tarba daga gwamnan jihar, Aminu Bello Masari da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli.
Daga nan jiga-jigan jam’iyyar mai mulki biyu suka garzaya zuwa gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin kai masa gaisuwar Sallah.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a yanzu haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
Mun dai ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC) a zaben 2023, Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaben mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta kuma rahoto cewa a yau Lahadi, 10 ga watan Yuli, za a bayyanawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar na mataimakin shugaban kasa a mahaifarsa ta Katsina.
Asali: Legit.ng