Liman Ya Yi Wa Kwankwaso Kamfen A Wurin Sallar Idi, Ya Ce Shine Dan Takara Mafi Cancanta a 2023
- Babban limamin masallacin Daawah da ke Kano, Sheikh Muhammadu Aminudeen ya ce Sanata Kwankwaso ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya a 2023
- Sheikh Muhammadu Aminudeen ya yi wa tsohon gwamnan na Kano addu'a ya kuma zaburar da shi ya cigaba da jajircewa don ganin ya yi nasara a zaben na 2023
- Babban malamin ya furta hakan ne yayin hudubar da ya yi a ranar Idi a masallaci inda Kwankwaso da wasu manyan yan siyasa suka hallarta
Kano - Sheikh Muhammadu Aminudeen, babban limamin masallacin Juma'a na Daawah, Kano, ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kara kaimi a yakin neman zabensa na shugabancin kasa.
Babban limamin, wanda da ne ga marigayi Sheikh Aminudeen Abubakar, shaharraren malamin addinin musulunci a Kano kuma wanda ya kafa Kungiyar Daawah ta Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da ya ke hudumar Eid-El-Kabir ga dubban masu ibada, ciki har da Kwankwaso, a ranar Asabar, limamin ya ce tsohon gwamnan na Jihar Kano "yana da dukkan halaye da ake bukata don jagorancin Najeriya kuma ya fi yan takarar APC da PDP."
Ya bayyana cewa Kwankwaso mutum ne mai matukar kaunar ganin cigaban Najeriya kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.
Sheikh din ya kara da cewa tsohon ministan tsaron makusanci ne ga marigayi Sheikh Aminuddeen wanda ya rasu a shekarar 2015.
Ya yi addu'ar Allah ya ceto Najeriya daga kallubalen tsaro da ke adabar ta a yanzu kuma ya jagoranci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara.
Dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP a zaben 2023 a Kano, Abba Kabir Yusuf da abokin takararsa Kwamared Aminu Abdussalam na cikin wadanda suka hallarci sallar idin.
Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP
A bangare guda, Rufai Ahmed Alkali, shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, na kasa ya ce kalaman da aka danganta da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, ba a fahimce su ba,Jaridar The Cable ta rahoto.
A ranar Asabar, Kwankwaso ya ce yana bawa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party, 'muhimmiyar dama' na zama mataimakinsa.
Asali: Legit.ng