Trela Ta Markade Mutum 8 Da Ragunan Sallah Masu Yawa A Wani Mummunan Hatsari

Trela Ta Markade Mutum 8 Da Ragunan Sallah Masu Yawa A Wani Mummunan Hatsari

  • Wani mummunan hatsarin mota da ya faru tsakanin manyan motocci biyu a Kwara ya yi sanadin mutuwar mutum 8 da shanu masu yawa
  • Lamarin ya faru ne a mahadar Okoolowo a karamar hukumar Ilorin ta Kudu misalin karfe 6 na safiyar ranar Laraba a cewar majiyoyi
  • Fredrick Ogidan, Kwamandan Hukumar Kiyayye Haddura na Jihar Kwara ya tabbatar da afkuwar hatsarin da ya ce ya ritsa da mutum 17, amma 8 suka mutu hudu kuma suka jikkata

Jihar Kwara - Mutane takwas da wani adadin shanu da ba a fayyace bane suka mutu bayan wani trela da ke tahowa daga arewacin Najeriya ya kutsa cikin wani mota da ake tsaye a Jihar Kwara.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne kusa da mahadar Okoolowo, karamar hukumar Ilorin Ta Kudu na jihar misalin karfe 6 na safen ranar Laraba kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Yadda wasu matan aure suka rasu a hadarin mota yayin da suke dawowa daga cefanen sallah

Hatsarin Mota a Kwara
Trela Ta Markade Mutum 8 Da Ragunan Sallah Masu A Kwara. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wani mazaunin unguwar, Salaudeen Abiola, direban motar dauke da shanu mai lamba DAT SGM396ZR ya kutsa wa wata trelan ne daka ajiye a titin.

Ya ce mutumin da abin ya faru da shi wanda ake kyautata zaton shine mai dabobin kuma ke tuka motar ya mutu nan take.

"Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da masu sayar da raguna da masu tireda da ke kusa da wurin. Abin babu dadin gani ko kadan," in ji shi.

Wani shaidan gani da ido na daban ya ce hausawa 10 da Yarbawa biyu na cikin wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa an kai gawarwakinsu wurin ajiya a Babban Asibitin Ilorin.

Hukumar FRSC ta Jihar Kwara ta tabbatar da hatsarin

Kwamandan Hukumar Kiyayye Haddura na Jihar Kwara, Fredrick Ogidan, ya tabbatar wa Daily Trust afkuwar lamarin a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

Ya ce:

"Mutum goma sha bakwai ne harin ya ritsa da su, amma 8 sun mutu yayin da 4 sun jikkata."

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

A wani rahoton, Dakta Sadiq Amali na sashin nazarin halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Jigawa ya bayyana cewa ya yi hasashen za a kai hari gidan yarin Kuje a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Yayin da ya ke magana kan harin a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Dakta Amali ya ce ya rubuta wasika ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbsola, game da yiwuwar kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164