Gwamnan Neja ya dakatar da ayarin motocinsa don ya taimaka wa mutanen da suka yi hatsari
- Yayin da yake kan hanyar komawa gidan gwamnati daga Abuja, Gwamna Neja ya tsaya taimaka wa wasu motoci da suka yi haɗari a Paiko
- Gwamna Abubakar Sani Bello, ya jajantawa mutanen da ke cikin motocin tare da ɗaukar nauyin yi wa masu rauni magani
- Ya umarci a kai masu raunin karaya Asibitin IBB Minna, sannan kuma ya sa a gyara motocin biyu duk daga asusun gwamnati
Niger - Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya dakatar da Ayarin motocinsa a garin Paiko, hedkwatar ƙaramar hukumar Paiko domin taimaka wa wasu mutane da suka yi haɗari.
Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa gwamnan ya nuna wannan halin jin ƙan ne yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gidan gwamnati bayan halartar wasu taruka a Abuja.
Haɗarin ya rutsa ne da wata Motar Marsandi 200 da ke ɗauke da iyalai yan gida ɗaya su biyar a kan hanayarsu ta zuwa Illorin, jihar Kwara da kuma wata motar haya maƙare da fasinjoji.
Mutum uku daga cikin fasinjojin motar sun samu raunin karaya yayin da ragowar mutum biyu suka ji raunuka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Haka zalika a ɗaya ɓangaren kuma, baki ɗaya mutum biyar da ke cikin Motar Marsandi 200 ba su ko kwarzane ba.
Wane taimako gwamnan ya ba mutanen?
Gwamna Bello, wanda ya jajantawa baki ɗaya mutane da haɗarin ya rutsa da su, ya umarci a ɗauki waɗan da suka karye a kai su babban Asibitin Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna domin yi musu magani.
Ya kuma umarci ɗaya daga cikin hadimansa da ke nan tare da shi, ya tabbatar an gyara motocin da suka yi haɗarin kuma daga asusun gwamnati.
Bugu da ƙari, gwamnan ya bukaci Ofishin yan sanda na Paiko su duba lafiyar direban motar da ta yi haɗarin, wanda ya kai kansa hannun yan sanda bayan aukuwar lamarin.
A wani labarin kuma Kwankwaso ya dira Osun don yaƙin neman zaɓen NNPP, ya ce APC da PDP ba su da bakin tunkarar mutane
Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyya mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso , ya ce jam'iyyar APC mai mulki da PDP duk sun gaza, don haka ya yi kira ga masu katin zaɓe su kaɗa wa NNPP kuri'unsu a zaɓen Osun da ke tafe.
Kwankwaso, wanda ya je Osun domin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan na jam'iyyarsa, ya roki mazauna jihar su fito kwansu da kwarkwata su kaɗa wa NNPP kuri'un su a ranar 16 ga watan Yuli, 2022.
Asali: Legit.ng