Mummunar gobara ta lashe rayukan ma'auratan likitoci a Maiduguri

Mummunar gobara ta lashe rayukan ma'auratan likitoci a Maiduguri

  • Gagarumar gobara ta lakume rayukan ma'aurata wadanda dukkansu biyun likitoci a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri
  • Kamar yadda ake kyautata tsammani, musabbabin gobara da ta lashe rayukan Dr Auta Gidado da Dr Amina, man fetur ne
  • An gano cewa Dr Auta yayi kokarin ceto matarsa da ta fara konewa, amma sai gobarar ta hada da shi inda ya rasy Talata, ta rasu Alhamis

Maiduguri, Borno - Gobara ta lakume rayukan wasu ma’auratan likitoci, Dr Auta Gidado da matarsa Dr Amina Ahmad.

Har zuwa mutuwarsu, su dukka suna aiki ne a karkashin asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Gobara ta halaka likitoci
Mummunar gobara ta lashe rayukan ma'auratan likitoci a Maiduguri. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a safiyar Lahadi a gidansu da ke Lagos Street, Maiduguri, kuma ana zaton fetur ne ya haddasa gobarar.

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

Wata majiya ta iyalin ta ce gobarar ta fara kona matar ne kuma a kokarin ceto ta ne mijin ya kone sosai inda aka kwashe su zuwa asibitin da suke aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma Dr Auta Gidado ya rasu a safiyar ranar Talata.

Majiyar ta bayyana cewa an binne marigayi Dr Auta Gidado daidai da koyarwar musulunci bayan an sallaci gawarsa a masallacin UMTH.

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Kasa da sao’i 24 bayan mutuwar mijin, mun kuma rasa Dr Amina Ahmad a safiyar yau (jiya). Mun samu sakon da misalin karfe 3:00am.”

Yayin da yake tabbatar da lamarin, Shugaban kungiyar likitocin UMTH, Dr Abdullahi Usman, ya nuna bakin ciki kan mutuwar ma’auratan.

Ya ce:

“Eh mun rasa su su biyun sakamakon gobara. Yanzu haka da muke magana, babu wanda zai iya baku cikakken bayani, amma abun da aka fada mana shine cewa gobarar ta barke ne daga fetur.”

Kara karanta wannan

Buhari ya sake nada Hajiya Saratu Umar a matsayin shugabar hukumar NIPC

Ya kara da cewa:

“Ina fatan mutane za su mutunta mamatan. Wannan lokacin bakin ciki ne a garemu mu takwarorinsu.”

Gobara ta kashe mutum 14 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

A wani labari na daban, 'yan gudun hijira 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da 15 daga ciki suka samu raunika daban-daban. Hakan ya faru ne sakamakon barkewar gobara a sansanin 'yan gudun hijarar da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gobarar ta fara ne da karfe 2:15 na yammacin ranar Alhamis a sansanin. Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, an yi kokari wajen kashe wutar da gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng