Hukuncin azumi a Juma'a idan ya yi kicibis da lokacin Ranar Arafah a Musulunci

Hukuncin azumi a Juma'a idan ya yi kicibis da lokacin Ranar Arafah a Musulunci

A wani faifan murya da yake yawo a dandalin sada zumunta, Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi gamsassshen bayani a game da ranar Arafah da azuminta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legit.ng Hausa ta saurari wannan faifai inda Shehin malamin na Musulunci ya fayyace sabanin da ake samu a game da hukuncin ware Ranar Juma’a da yin azumi

A wannan jawabi, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi magana a kan darajar Arafah da kuma yin azumi ga wadanda ba su samu ikon zuwa yin hajji ba

Mutanen da ke gida za su samu wannan falala ta ranar Arafah, don haka Shehin ya ce Musulunci ya shardanta yin azumi a wannan rana, wanda yake da dinbin lada.

Hadisi ya zo daga bakin Manzon Allah (SAW), yana cewa azumin Arafah yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da kuma zunubin wata shekarar da za ta zo.

Kara karanta wannan

Hukumar yansanda ta karyata zargin kai wa cocin Anambara hari da Fulani suka yi

Ga Arafah ga Juma'a a 1443

Sai dai a wannan shekara ta 1443 (watau 2022), Arafah ta fado ne a ranar Juma’a, kuma Manzon Allah (SAW) ya yi hani a kan kebe Juma’a ita kadai da yin azumi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu su na ganin tun da azumin bana ya fado a ranar Juma’a, to ba zai halasta ayi azumin ba, ko kuma akalla sai an hada Alhamis (tun da Asabar za ta zama idi).

Ba a kebe Juma’a da ibada

Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya ce lallai Malamai sun ce Manzon Allah (SAW) ya haramta kebe daren Juma’a da sallah ko yinin da wani azumi.

A cewar Dr. Rijiyar Lemu, hanin yana magana ne a kan mutum ya ware ranar ta Juma’a saboda kurum ta na Juma’a, ya yi ibada, yace hakan karara ba daidai ba ne.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Ranar Arafah a Musulunci
Masu aikin Hajj Hoto: Twitter / Allahu Akbar
Asali: Twitter

Ga wanda wani azumi na sunnah ya fado a ranar Juma’a, zai azumce shi saboda wannan sunnar.
Kamar wannan lokaci da azumin Arafah ya fado a cikin Juma’a, ba zai shiga cikin hanin ba, saboda mutum bai kebe wannan yini saboda azumin Juma’a ba.
Kuma ko wace rana Arafah ta fado, haka zai azumce ta, ba don ranar ba (sai domin ta na Arafah).

- Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu

Malamin ya ce lafazin da Muslim ya kawo na hadisin ya gaskata haka, Annabi (SAW) ya yi nuni ga cewa mutum zai iya yin duk azumin da ya saba ko a ranar Juma’a.

Misali mai yin azumin Annabi Dawuda (AS) ko Sitta Shawwal ko Ashura zai iya azumtar Juma’a idan ta kama ko da kuwa mutum bai hada da Alhamis ko Asabar ba.

Wannan shi ne irin bayanin da mu ka ji ya fito daga bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kwanan nan.

Kara karanta wannan

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

Malaman sun ce magabata kamar Ibn Hajar Al Asqalani a Fatahul Bari da Ibn Qudama a littafinsa Al Mughny da su Abdallah Bn Baaz sun tafi kan wannan ra’ayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng