Tawagar shugaban kasa basu tabuka komai ba a lokacin da yan bindiga suka auka masu – Mazauna kauyukan Katsina
- Tawagar shugaban kasa basu tabuka komai ba a lokacin da yan bindiga suka auka masu a ranar Talata a jihar Katsina
- Wannan shine sabon bayanin da ke fitowa da wasu mazauna kauyukan jihar da abun ya wakana a idanunsu
- Tawagar sun tsaya a kauyen Turare sannan sun ci gaba da tafiyarsu bayan sun tabbatar da cewar maharan sun yi nisa daga inda suke
Katsina - Sabbin bayanai da ke fitowa daga wasu mazauna kauyukan Katsina kusa da inda aka farmaki tawagar shugaban kasa a ranar Talata sun nuna cewa jami’an tsaro da ke cikin ayarin basu yi musayar wuta da yan ta’addan ba, don haka maharan sun tsere ba tare da rauni ba.
Wani ganau ya shaidawa Daily Trust cewa maharan sun farmaki wani kauye mai suna Buturkai inda suka tarwatsa jama’ar gari, lamarin da ya tilasta masu komawa kauyen Turare inda harin ya gudana, sannan wasun su suka je Shandai, wani wurin kiwo.
Ya bayyana cewa hakan ya faru ne kafin isowar tawagar shugaban kasar.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A Buturkai, yan bindigar sun kashe mutane uku sannan suka je kauyen Dogon Ruwa inda suka kashe mutum biyu, sannan suka fasa shaguna da dama suka kwashe kayayyaki kafin suka isa kauyen Marke inda suka yi fashin wasu dabbobi."
Ya ce a lokacin da tawagar suka isa Turare sannan suka gano abun da ke gudana, sai suka ajiye ababen hawansu a makarantar Firamare ta LEA da ke kauyen na dan lokaci, suka yi wasu bincike sannan da suka gano cewa yan bindigar sun yi nisa.
Daga nan sai suka ci gaba da tafiyarsu, yayin da suke ta harbi a iska har suka wuce wajen da ke da hatsarin.
Wani mazaunin Marke, inda yan bindigar suke a lokacin da tawagar ta iso, ya ce:
“Bayan yan bindigar sun bar kauyenmu da dadewa ne ayarin jami’an tsaro (tawagar shugaban kasar) suka iso, suna ta harbi a iska.
“A fahimtarmu, wadannan yan bindigar da suka kashe kwamanda a yankin Zakka ne suka bi ta Kwanar Dutse zuwa Kunamawar Mai Awaki inda suka kashe mutane biyu, sannan Kunamwa Babba, sun kashe mutane biyu ma a nan, wanda daya daga cikinsu mijin sirikata ce.”
Ya kara da cewa wadannan yan bindigar ne suka karasa Unguwar Gurbai inda suka kashe mutane shida sannan Doguwar Dankwambo inda suka kashe mutane biyu da kuma Unguwar Ido inda suka kashe mutane shida.
Wanda aka yi a idonsa, ya bada labarin yadda Miyagu suka aukawa Ayarin Shugaban kasa
A baya mun ji cewa, wani mazaunin garin Katsina wanda aka kai wa tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari hari a gabansa, ya bada labarin yadda ya sha da kyar.
Wannan Bawan Allah ya shaidawa Daily Trust cewa daji suka ruka ruga domin tsira da ransu.
A cewar wannan mutumi wanda abin ya kusa rutsawa da wasu, shi da wasu Bayin Allah sun boye ne a cikin jeji domin gudun ‘yan bindigan su auka masu.
Asali: Legit.ng