Tsagwaron basira: Yadda yarinya 'yar Najeriya ke samar da haske daga ruwa da gishiri

Tsagwaron basira: Yadda yarinya 'yar Najeriya ke samar da haske daga ruwa da gishiri

  • Wani faifan bidiyo na wata hazikar yarinya mai samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da wayoyi da kofin ruwa da gishiri ya bayyana a shafukan sada zumunta
  • Bidiyon ya nuna yarinyar ‘yar Najeriya a zaune a kasa a daki yayin da take wani siddabarun samar da wutar lantarki
  • Bayan ta gama hade-haden, sai ta sanya wata 'yar waya a cikin kofin ruwa kuma nan da nan sai ga haske wal

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata karamar yarinya ta yadu a shafukan sada zumunta bayan da ta nuna sabuwar fasahar da ta koya mai ban mamaki.

A cikin wani gajeren bidiyo, yarinyar da aka gani zaune a daki, ta ce tana son nuna yadda ta samar da wutar lantarki ta ruwa da gishiri.

Yarinyar hazika ta zauna ta fara yin wani abu kamar almara a gaban mahaifiyarta, sai kuwa ga abin mamaki.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

'Yar Najeriya na samar da wuta daga gishiri da ruwa
Tsagwaron basira: Yadda 'yar Najeriya ke samar da haske da ruwa da garin gishiri | Hoto: @chychido2
Asali: UGC

Ta yi amfani da wasu 'yan wayoyi, kwan haske, da wasu abubuwan da ta hada tare a cikin bidiyon kuma nan da nan ya fara haska dakin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da mahaifiyarta ta ga hasken, ta yaba mata, yarinyar ta yi murmushin cikin farin ciki. An yada bidiyon ne akan wani akant na TikTok mai suna @chychido2.

Kalli bidiyon:

'Yan TikTok sun yi ca kan bidiyon

Yarinyar ta samu yabo a shafin na yanar gizo bayan da bidiyon ta ya bayyana.

@calmejenny118 ya ce:

"Nan kusa nepa za su fara kukan rashin waya nan da 1 bayan wata karamin yarinya ko ma mutum ne ke samar da haske daga ruwa don haka, ko dai ido na ne ke ciwo."

@oluwamezie0 ya ce:

"Makaranta dai ba damfara bane, ku kuka halarci makarantar gama-gari kuma laga-laga.. kin burge yarinya."

Kara karanta wannan

Hukumar yansanda ta karyata zargin kai wa cocin Anambara hari da Fulani suka yi

@joex078 yayi sharhi da cewa:

"Kar dai Najeriya tazo ta canja mata mafarki zuwa zama lauya. Na tuna lokacin da na fara girma da kaunar kwallon kafa amma yanzu gani sai latsa kwamfutar tafi da gidanka nake."

@specialking4 ya ce:

"Me yasa ta yi amfani da baturi, in gishiri da ruwa ne kawai zai yi aikin? ina tambaya a matsyain dalibi."

Gwana ta gwanaye: Mai hijabi ta girgiza intanet yayin da ta nuna kwarewa a kwallon kafa

A wani labarin, a kwanan nan ne aka dauki bidiyon wata budurwa ‘yar Najeriya, inda ta yadu a shafin Instagram tana buga wasan kwallon kafa daidai iyawarta.

Bidiyon ya baiwa jama'a mamaki a shafukan sada zumunta inda suka yi ta cancara mata yabo kan bajintar iya kwallon kafa.

A cikin faifan bidiyon da ta wallafa ta shafinta na Instagram mai suna @hijabballer, an gan ta tana sanye hijabi kuma tana tsalle-tsalle a lokacin da take nuna kwarewarta.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Asali: Legit.ng

Online view pixel