Tashin hankali: Dukkan kasurguman 'yan Boko Haram da ke daure a Kuje sun tsere, inji minista
- Ministan tsaro na Najeriya ya fito ya yi bayani, ya bayyana abin da ya faru a gidan yarin Kuje a daren jiya Talata
- Ya kuma shaida cewa, ana zargin 'yan Boko Haram ne suka saki 'yan uwansu da ke daure a magarkamar
- A bangare guda, jami'an tsaro na ci gaba da aikin tattaro sauran fursunonin da suka tsere a yayin harin
Kuje, Abuja - Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce dukkan wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne a gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayya (FCT) sun tsere.
Ministan ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai a cibiyar da ke Abuja, inji rahoton TheCable.
Idabn baku manta ba, ‘yan bindiga sun kai hari gidan yarin, inda suka dasa nakiyoyi da ababen fashewa a daren ranar Talata.
Shuaib Belgore, sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin cikin gida, ya ce maharan sun zo gidan yarin cikin “kyakkyawan shiri” dauke da bama-bamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin garin ya shaidawa jaridar cewa, an shafe sama da mintuna 30 ana jin karar harbe-harbe, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin.
Duk 'yan Boko Haram sun tsere, inji Bashir Magashi
Magashi ya ce maharan ’yan Boko Haram ne kuma an nemi mambobinsu 64 da suke daure a magarkamar an rasa.
The Nation ta ruwaito ministan na cewa:
“Abin da ya faru a zahiri, sun zo cikin adadi mai yawa kuma sun saki wasu daga cikin fursunonin. Yanzu muna kokarin gano irin fursunonin da suka saka.
“Muna kokarin ganin abin da za mu iya yi don ganin an dawo da duk wadanda suka tsere a gidan yarin zuwa farfajiyar magarkamar.
Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG
“Kusan fursunoni 994, muna da kusan 600 a ciki yanzu. An sake kamo mutane da yawa. Mutanen da suka zo yin haka daga bayanan da muka samu suna cikin wata kungiya ce ta musamman, daga dukkan alamu 'yan Boko Haram ne.
“A halin yanzu ba mu iya gano ko daya daga cikinsu ba. A halin yanzu, kusan 64 daga cikinsu a matsayin fursunoni kuma ba mu iya gano su ba.”
A halin yanzu dai jami’an tsaro na ci gaba da aikin bincike tare da tallafa wa sojojin sama domin kamo fursunonin baki daya.
An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga
A baya kunji cewa, da alamu wasu manyan fursunoni a gidan yari na Kuje da ke Abuja sun tsere a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata, inji rahoton The Nation.
Harin da ya dauki tsawon sa'o'i kadan, an ce jami'an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.
Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da abokan harkallarsa da ke wurin, mai yiwuwa sun tsere daga magarkama.
Asali: Legit.ng