Duk da makudan kudin da ake kashewa an kasa samun tsaro a Najeriya

Duk da makudan kudin da ake kashewa an kasa samun tsaro a Najeriya

  • Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam a katsina sun nemi gwamnati ta musu bayani akan yadda ake kashe makudan kudin tsaro
  • Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun bayyana bacin ran su akan babban kwamandan yan sanda da yan bindiga suka kashe a Katsina
  • Abdulrahman Abdullahi ya ce lokaci yayi da yakamata jam'ian tsaro su rika kaiwa yan bindiga hari a inda suke

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jiahr Katsina - Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam a katsina sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta musu bayani akan makudan kudaden da ake kashewa a harkar tsaro dan ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Rahoton jaridar PUNCH.

Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne a ranar Talata da suke tsokaci akan kisan babban Dansandan ACP Aminu Umar, da yan bindiga suka kashe a jihar.

Kara karanta wannan

Hukumar yansanda ta karyata zargin kai wa cocin Anambara hari da Fulani suka yi

Gamayyar Kungiyoyin a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shugabanta na Katsina, Abdulrahman Abdullahi, ta koka akan kisan kwamandan rundunar yan sandan, inda ya jaddada cewa lamarin ya nuna gazawar harkar tsaron Najeriya.

buhari
Duk da makudan kudin da aka kashewa an kasa samu tsaro a Najeriya ; FOTO LEADERSHIP
Asali: Facebook
A jawabin ya kara da cewa, “Abin takaici ne yadda gwamnati ta kasa samar wa jami’an tsaro kayan aiki da kuma rashin fatattakar ‘yan bindiga daga yankunansu na ci gaba da zama sanadin asarar jami’ai irinsu ACP Aminu Umar da sauran ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A kowani rana yan ta’addan nan suna kara yin karfi ne, Ya kamata a kai fadar inda suke, ta hanyar amfani da sojojin kasa da na sama. Amma abin takaicin shi ne, sojojin sama da sojojin kasa ba sa kai farmaki da karfin da ake bukata.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Za ku ga jiragen yaki suna shawagi a sararin sama amma idan kun nemi yan ta’addan da aka kashe sai aka sa nunawa. Yan bindiga na kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba hari a wuraren dake kusa da sansanonin soji amma ba sa kai dauki.
” kullum Ana kashe makudan kudi a harkar tsaro amma lamarin yana kara ta’azzara. Lokaci ya yi da Shugaban kasa da yan Majalisar Dokoki ta kasa su fara tambayar dalilin da ya sa ba a samun sakamako mai kyau. Dole ne a daina wannan kashe-kashen na rashin hankali"inji shi.

Babu wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a cocin Anambra – ‘Yan sanda

A wani labari, Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta karyata rahoton da aka wallafa a Facebook cewa wasu Fulani hudu sun kutsa cikin cocin Awada Grace na God a ranar Lahadi da nufin tayar da bam a cocin kamar yada jaridar Daily Trust ta rawaito.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamna a Kaduna ya hada kai da 'yan Shi'a don nemawa Peter Obi kuri'u

Hukumar yansanda a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya ta bakin kakakinta, DSP Ikenga Tochukwu, ta ce labarin kanzon kuregen da aka wallafa Facebook, an yi shine domin a haifar da tashin hankali da kiyayyar kabilanci da na addini a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa