Peter Obi: Ba Abin Da Zai Hana Ni Cire Tallafin Man Fetur Idan Na Zama Shugaban Kasar Najeriya

Peter Obi: Ba Abin Da Zai Hana Ni Cire Tallafin Man Fetur Idan Na Zama Shugaban Kasar Najeriya

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya ce zai cire tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa
  • Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya koka kan yadda Najeriya ke kashe kudi a kan tallafi fiye da bangaren ilimi da lafiya
  • Obi ya ce Najeriya ta kashe fiye da Dallan Amurka Miliyan 40 kan biyan tallafin man fetur cikin shekaru 10 da suka shude kuma ba amfanar da yan kasa abin ke yi ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ya lashi takobin cire tallafin man fetur kuma ya juya akallar tattalin arzikin zuwa wasu bangarorin idan an zabe shi shugaban kasa a zaben 2023.

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya ke amsa tambayoyi daga mai gabatar da shirin Morning Show, na Arise TV, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

Peter Obi
2023: Peter Obi Ya Lashi Takobin Cire Tallafin Man Fetur Idan Ya Zama Shugaban Najeriya. Hoto: @nigeriantribune.
Asali: Twitter

Ya ce kudaden da gwamnatin tarayya ke kashe wa kan ilimi da kiwon lafiya ba su kai kashi 50 cikin 100 na abin da ta ke kashewa ba a tallafin man fetur, wanda ya ce baya taimakawa wurin gina kasa.

"A shekaru 10 da suka wuce, tallafin man ya kai $40 biliyan. Bututu ne da ke nutsewa. Hakan na nufin; mun kashe fiye da $40 biliyan kan tallafin mai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jimillar abin da muka kashe kan ilimi a shekaru 12 da suka gabata ya kai N8 tiriliyan. Don haka, a shekaru 10 kimanin $8 tiriliyan 8."

Obi ya ce babu yadda kasa za ta cigaba idan aka mayar da muhimman bangarori kamar lafiya da ilimi koma baya a kan tallafin man fetur.

2023: Idan Har Ka Ajiye Okowa, Ba Zaka Samu Kuri'an Igbo Ba, Matasan Ohanaeze Sun Gargadi Atiku Da PDP

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

A wani rahoton, matasan Igbo karkashin kungiyar Ohanaeze Ndigbo Youth Council Worldwide, OYC, ta gargadi dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar kan duk wani shiri na ajiye Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.

A cikin da shugabannin kungiyar suka raba wa yan jarida a ranar Talata, ta ce idan Atiku ya ajiye Okowa, duk abin ya faru, shi ya janyo, rahoton Vanguard.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban OYC na kasa, Mazi Okwu Nnabuike da Sakatarenta, Obinna Achionye ta ce duk wani yunkuri na canja Okowa ba zai haifar da alheri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164