Najeriya ta shiga cikin matsanancin hali inji Peter Obi

Najeriya ta shiga cikin matsanancin hali inji Peter Obi

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce Najeriya tana cikin matsanancin hali dake bukatar kwararre irin shi ya jagorance ta
  • Obi ya ce sama da ‘yan Najeriya miliyan 100 sna cikin talauci saboda yadda wasu manyan Najerya ke Tunani
  • Buba Galadima yayi fatali da zargin cewa siyasar Kudu-maso-Gabas ba ta da karfin siyasar Kwankwanso

Jihar Anambara - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce a halin yanzu Najeriya na cikin rudani kuma tana bukatar kwararru irinsa domin ceto rayuwarta.

Obi ya yi wannan jawabi ne a wani shirin ‘The Morning Show’ a gidan talabijin na Arise, inda ya yi jawabi a kan tambayoyin da ke tattare da dambarwar dake tsakanin jam’iyyarsa da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party. Rahoton PUNCH

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

A baya dai jaridar PUNCH ta ruwaito yadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwakwanso, ya bayyana cewa ba zai ja baya ba wajen karbar tikitin mataimakin shugaban kasa, yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da neman hadin kai domin ganin an dade ana tattaunawa kan yiwuwar kawance.

PETER
Najeriya ta shiga cikin halin kakanikayi inji Peter Obi; FOTO Legit.NG
Asali: UGC

An kuma ruwaito cewa, wani jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi fatali da kalaman da aka ce Kwankwaso yayi a baya na cewa NNPP ba za ta taka rawa na biyu a tikitin tsayawa takara ba bisa hujjar cewa Kudu-maso-Gabas ba ta da karfin siyasar Kwankwaso kamar yadda jaridar NewsNGR ta rawaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani kan kalaman jam’iyyar NNPP, Obi ya ce ‘yan Najeriya miliyan 100 ne ke cikin talauci a yau saboda irin tunanin wasu daga cikin manyan kasar irin sa.

Kara karanta wannan

'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

Ya kuma bayyana Najeriya a matsayin mai jinya da ke cikin halin kakanikayi, wanda zai mutu a take in bai samu kulawar kwararren masani irin sa ba.

Da yake rokon ‘yan Najeriya da su yi watsi da siyasar addini da kabilanci, obi ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya ya kamata su zabi shugabanninsu bisa cancanta.

Harin gidan yarin Kuje: Dole ne a sauya fasalin tsaron Najeriya – Falana

A wani labarin kuma, Abuja : Wani dan kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya yi kira da a sake duba tsarin tsaron Najeriya bayan harin da yan bindiga suka kaiwa gidan yari Kuje dake birnin Abuja. Rahoton DailyTrust

Falana, Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya gana da gidan talabijin na Channels Tv cikin shirin Sunrise Daily a safiyar Laraba, ya ce babu wanda ya tsira a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa