Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga
- Majiyoyi sun shaida cewa, an nemi DCP Abba Kyari da 'yan tawagarsa a gidan yarin Kuje an rasa biyo bayan harin 'yan bindiga
- Rahotanni sun ce, haka nan wasu jiga-jigan da ke tsare a cikin magarkamar duk sun yi batan dabo a harin
- Idan baku manta ba, jiya ne aka samu wani mummunan yanayi na harin magarkamar Kuje, akalla mutane 600 sun tsere
Kuje, Abuja - Da alamu wasu manyan fursunoni a gidan yari na Kuje da ke Abuja sun tsere a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata, inji rahoton The Nation.
Harin da ya dauki tsawon sa'o'i kadan, an ce jami'an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.
Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da abokan harkallarsa da ke wurin, mai yiwuwa sun tsere daga magarkama.
Shi ma haka tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da takwaransa na Taraba Jolly Nyame da majalisar kasa ta yi wa afuwa a baya-bayan nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da sakin su Dariye ba har aka samu akasi aka kai hari magarkamar.
Majiyoyi a cikin magarkamar sun shaidawa jaridar cewa baya ga manyan fursunonin, wasu 'yan ta'adda da sauran masu laifi sun tsere yayin da maharan ke luguden wuta.
Sai dai har zuwa lokacin da hada wannan rahoto, babu wani tabbaci a hukumance kan adadin wadanda suka tsere da bayanansu, haka nan BluePrint ta ruwaito.
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa zai yi wuya a iya tabbatar da ko an kwashe Kyari da mutanensa domin kare rayukansu kafin maharan su samu shiga wurin.
Majiyar ta kuma ce haka nan ga tsofaffin gwamnonin da ke daure a magarkamar.
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gyaran fuska ta Najeriya, Francis Enobore da karamin jami’insa, Mista Humphrey Chukwuendo.
Wani jami’in da ya so a sakaya sunansa ya ce har ya zuwa karfe 09:30 na safe ba a san inda Kyari yake ba, rahoton Punch.
Ya ce:
"Na tabbata bai bace ba kuma bai tsere ba. Amma ban san ainihin inda yake ba.”
Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar kimanin fursunoni 600 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje biyo bayan harin da wasu yan ta’adda suka kai a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Yuli, Channels TV ta rahoto.
A yayin wata ziyara da ya kai cibiyar, sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Mista Shuaibu Balgore, ya yi bayanin cewa an dawo da fursunoni sama da guda 300 kuma wasu na kan hanya.
Ya kara da cewar cibiyar na dauke da fursunoni 994 kuma cewa maharan, wadanda yake zaton yan Boko Haramn ne sun farmaki cibiyar don kubutar da abokan harkarsu, rahoton PM News.
Asali: Legit.ng