Ma'aikatan INEC Sun Rufe Kwamishina a Ofishinsa Saboda Rashin Biyansu Hakokinsu
- Ma'aikatan zabe a Jihar Abia sunyi zanga-zanga har sun rufe kwamishinan INEC na jihar a ofishinsa saboda hakokinsu
- Daya daga cikin masu zanga-zangan da ya nemi a boye sunansa ya ce cikin kudaden har da na zaben fidda gwani na jam'iyyu da aka yi a baya-bayan nan
- Kakakin INEC na jihar, Mr Bamidele Oyetunji ya ce matsala ne na cikin gida, kuma an warware matsalar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Abia - Ma'aikatan hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, reshen Jihar Abia sun rufe kwamishinan INEC, mai kula da jihar, Joseph Iloh, a ofishinsa kan rashin biyansu hakokinsu.
Masu zanga-zangar, a ranar Talata, sun tare kofa fita daga hedkwatar INEC da ke kallon Babban Bankin Najeriya na Umuahia a ranar Talata, rahoton Vanguard.

Source: UGC
Sunyi amfani da babban motarsu na ma'aikata sun rufe kofar hedkwatar suna mai cewa Kwamishinan ba zai bar ofishinsa ba zai ya biya su dukkan hakokinsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamishinan zai yi ritaya daga aiki nan da yan makonni.
A cewar daya daga cikin masu zanga-zangar da ya nemi a boye sunansa, ya ce wasu daga cikin hakokinsu har da kudin zaben fidda gwani na jam'iyyun siyasa da aka kammala a baya-bayan nan.
An yi kokarin ji ta bakin kwamishinan game da afkuwar lamarin amma ba a same shi ba a lokacin hada wannan rahoton.
Martanin hukumar INEC ta Abia
Jami'an hulda da jama'a na INEC a jihar, Mr Bamidele Oyetunji ya ce matsala ne na cikin gida, kuma an warware matsalar.
Zaben 2023: Ba Zan Yi Wa INEC Katsalandan Ba, In Ji Buhari
A wani rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jadada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta yi zabe na adalci kuma cikin zaman lafiya a 2023.
Ya bada tabbacin cewa ba zai yi wa INEC katsalandan ba, yana mai cewa bayan kammala zaben cikin gida na jam'iyyu, yanzu an sa ido ne kan zaben 2023 a Najeriya.

Kara karanta wannan
Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin gano yawan 'Yan Najeriya
Buhari, a cewar sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter, ya yi magana ne a daren ranar Laraba a Lisbon yayin ganawarsa da yan Najeriya da ke zaune a Portugal.
Asali: Legit.ng
