Yanzu-yanzu : Limamin Katolika da aka yi garkuwa da shi ya samu 'yanci
- Limamin cocin Katolika da akayi garkuwa da shi a ranar Litinin ya samu yanci daga hannun yan bindga
- Shugaban cocin Katolika na Kafanchan Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya bayyana farin cikin sa game da sako Fada Emmanuel Silas da yan bindiga sukayi
Jihar Kaduna - Bisanin cika awanni 24 da sace shi, wani limamin cocin Katolika na Kaduna, Reveren Fada Emmanuel Silas, ya samu 'yanci daga hannun yan bindigan da suka yi garkuwa dashi kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta rawaito.
Shugaban jam’iar cocin katolika na Kafanchan, Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da sakin Faston a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Kaduna.
A ranar Litinin ne aka yi garkuwa da Fada Silas a makarantar St. Charles Catholic Church Zambina a karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna rahoton jaridar The Guardian.
Yanzu-Yanzu: 'Yan Sa'kai sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a Filato, rayuka sama da 10 sun baƙunci lahira
Shugaban jami’ar ya ce,
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“zukatan su a cike yake da farin ciki, kuma sun mika yabo da godiya ga Ubangiji da babbar murya yayin da suke sanar da dawowar dan’uwansu, Rev. Fr. Emmanuel Silas, wanda yan bindiga suka sace a cocin St. Charles Catholic Church, Zambina dake karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna, da sanyin safiyar ranar 4 ga watan Yuli, 2022.
“ An sako shine da misalin karfe 9.00pm na safiyar ranar Litinin kafin cikia awanni 24 da yin garkuwa da shi," inji shi.
Gwamnatin tarayya ta yi gaggawar zargin ISWAP Kan Harin Cocin Owo - Akeredolu
A wani labari, Jihar Ondo : Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sake kin amincewa da gwamnatin tarayya akan wanda ya dace a dorawa alhakin kashe masu ibada a garin Owo.
Da yake jawabi akan kisan, a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Channels Television's, ya ce alakantar da harin cocin Owo ga kungiyar ISWAP ya nuna akwai lauje acikin nadi. Rahoton ChannelsTV.com
Asali: Legit.ng