Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake sace wani babban fasto a Kaduna

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake sace wani babban fasto a Kaduna

  • A sa'o'in farko na ranar Litinin, miyagun 'yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani fasto mai suna Rabaren fada Emmanuels Silas a Kauru ta jihar Kaduna
  • Shugaban cocin katolika na Kafanchan, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo ne ya sanar da hakan cike da takaici da kunar rai ga manema labarai
  • A yayin kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu tare da gujewa daukar doka a hannu, yace zasu bi duk wata halastacciyar hanya ta kubutar da faston

Kauru, Kaduna - 'Yan ta'adda a sa'o'in farko na ranar Litinin sun sake yin garkuwa da wani limamin cocin katolika, Rabaren Fada Emmanuel Silas a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Shugaban Catholic Diocese ta Kafanchan, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da hakan a wata takardar da ya bai wa manema labarai a Kaduna, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo

'Yan bindiga
Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake sace wani babban fasto a Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Idan za a tuna, 'yan ta'adda sun halaka Rabaren Fada Vaishima Barogo a gonarsa dake Kujama, kan babban titin Kaduna zuwa Kachia a ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2022 kuma an birne shi a ranar 30 ga watan Yunin 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban cocin ya ce, "Cike da kunar rai muke sanar da garkuwa da aka yi da limaminmu, Rabaren Fada Emmanuel Silas. Lamarin ya auku a ranar 4 ga watan Yulin 2022 lokacin da muka fuskanci bai halarci bautar safe ba.
"An sace shi a iklisiya ta cocin katolika ta St. Charles dake Zambina a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
"Muna barar tsananin addu'ar saurin fitowarsa cikin koshin lafiya. Muna kira ga kowa da kowa da a kiyaye daukar doka a hannu.
"Za mu yi amfani da duk wata halastacciyar hanyar wurin tabbatar da sun sako shi lafiya cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

"Muna fatan yesu da ya sadaukar da rayuwarsa, zai saurari addu'o'inmu tare da tabbatar gaggawar sakin limaminmu da sauran wadanda aka yi garkuwa da su."

Kwanaki 3 da sace Fastoci 3, Miyagu sun yi garkuwa da Shugaban kungiyar Kiristoci

Awani labari na daban, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kungiyar Kiristoci watau CAN na reshen karamar hukumar Jos ta gabas da ke jihar Filato.

Rahoton da mu ka samu daga The Nation ya nuna an dauke James Kantoma ne da tsakar dare zuwa safiyar jiya, ranar Litinin 13 ga watan Yuni 2022. James Kantoma shi ne babban Faston cocin St. Anthony Parish da ke kauyen Angware, garin Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng