Rashawa: Ba a gama da AGF da ya saci biliyoyi ba, an maye gurbin wanda aka nada a kujerarsa
- Rahotanni sun ce an kori sabon mukaddashin Akanta-Janar na kasa Chukwuyere N. Anamekwe
- A cewar wata majiya mai tushe, an maye gurbinsa da Okolieaboh Ezeoke Sylvis, tsohon daraktan TSA
- Majiyar ta bayyana cewa an tsige Anamekwe daga mukaminsa ne saboda binciken da hukumar EFCC ke yi akansa
Abuja - Gwamnatin tarayya ta maye gurbin Mista Chukwuyere N. Anamekwe a matsayin mukaddashin Akanta Janar na tarayya (AGF), kamar yadda rahotanni suka bayyana a karshen mako.
An maye gurbinsa ne makonni biyu da suka gabata da wani, AGF Mista Okolieaboh Ezeoke Sylvis, tsohon Daraktan TSA (Asusun bai daya na tarayya).
The Nation ta gano cewa maye gurbin Anamekwe ya biyo bayan zargin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ke bincikensa akai.
An kuma tattaro cewa gwamnati ba ta ji dadin yadda ya bayyana cewa tana kinkimo bashi domin biyan albashi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda aka nada shi
An nada Anamekwe a matsayin mukaddashin AGF ne a ranar 22 ga watan Mayu. Ya yi wannan tsokaci mai cike da cece-kuce kan bashin da gwamnati ta karbo don biyan albashi a ranar 14 ga watan Yuni.
An ruwaito cewa, mista Sylva ya yi murabus daga ofis a farkon kwata na 2023.
Wata majiya ta shaida wa jaridar The Nation cewa, gwamnatin tarayya ta fara nemo sabon AGF da ya dace.
Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta Tarayya (HoCSF), Misis Folasade Yemi-Esan ta ba da sanarwar da bayyana hakan.
Ahmed Idris: EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar Da Ake Zargi Da Wawure N170bn
A wnai labarin, Hukumar Yaki da Rashawa da Masu Yi Wa Arzikin Kasa Ta'annati, EFCC, ta sako dakataccen Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris da ta kama kwanakin baya, Daily Nigerian ta rahoto.
Wasu majiyoyi daga iyalan Ahmad sun tabbatarwa Daily Nigerian da sakinsa inda suka ce a daren ranar Laraba aka sako shi.
Jami'an hukumar EFCC, a ranar 16 ga watan Mayu ne suka kama Mr Idris kan zarginsa da hannu wurin karkatar da kudade da adadinsu ya kai Naira Biliyan 80.
Asali: Legit.ng