Duk daya muke : Kristoci sun taya musulmai cire ciyayi a masalacin Kaduna.
- Mabiya addinin Krista sun taya musulmi cire ciyayi a masallacin idi a karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna
- Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yaba da taimakon cire ciyawa a masalacin idi da matasan Kristoci suka taya Musulmi yi
- Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) tayi kira da Musulmi da Kristoci sun rungumi juna su zauna lafiya ganin yadda jihar ke fama da rikin addini da kabilanci
Jihari Kaduna - Wasu mabiya addinin Kirista a karamar hukumar Kachia dake kudancin jihar Kaduna sun taya musulmi yanke ciyawa a wani masallaci da ake yin sallar idi.
Mista Daniel Bitrus, shugaban tawagar kristocin da suka ta ya musulmi gudanar da wannan aikin, ya ce sun yi hakan ne domin karfafa zumunci, hakuri da zaman lafiya da juna.
Tare suka yanke ciyawa da kawar da sharar dake harabar masallacin, wanda aikin ya dauke so kwana biyu suna yi kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
“Mun zo nan ne don tallafa wa ’yan’uwanmu wajen yanke ciyayi da kuma share dattin da ke cikin masallacin da kewaye, da nufin samar da zaman lafiya da hadin kai,” inji shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kuma zamu cigaba da yin haka a kowani shekara dan samu zaman lafiya tsakanin addinan biyu.
Da yake jwabi, Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), reshen karamar hukumar Kachia, Malam Ibrahim Tasiu, ya bayyana jin dadinsa kan yadda mabiya addinin kirista suka fito a taya su aiki.
Ya bayyana cewa matasan kiristoci sun riga musulmi zuwa filin Idin domin yin aikin.
Ya yaba da wannan matakin, inda ya ce wannan shi ne irinsa na farko a tarihin yankin Kudancin Kaduna, wanda ke yawan fuskantar rikicin kabilanci da na addini.
Ibrahim ya yi kira ga Musulmi da Krista da su zauna lafiya da juna.
Peter Obi baya kyamar mutanen arewa, karya ake masa: Inji hadimin sa
A wani labarin : Mai Magana da yawun bakin dan tankarar shugabankasa a jam’iyyar Labour party LP, Mista Peter Obi, ya musanta rahoton dake nuna maigidansa mai tsaurin ra'ayin addini ne kuma yana kyamar mutanen arewa.
Valentin Obienyem, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce wasu kungiyoyi da ba’a san su ba, wadanda ‘yan adawar siyasa ke daukar nauyinsu, ke yada karya kan Obi saboda karuwar farin jininsa.
Asali: Legit.ng