Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

  • Mabiya addinin kirista a jihar Kaduna sun taru domin taya musulmi ayyukan babbar sallah a tsakanin Asabar da Lahadi
  • Wannan na zuwa ne daga yankin Kachia, inda aka sha samun rikice-rikice na addini da kabilanci a jihar
  • Shugabannin yankin sun magantu kan manufar wannan hobbasa, inda suka yi kira da a zauna lafiya da kaunar juna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kachia, Kaduna - Wasu mabiya addinin Kirista a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna sun bi sahun musulmi wajen sare ciyawa a wani filin da ake sallar idi a lokacin Sallah.

Mista Daniel Bitrus, shugaban tawagar ‘yan agajin da suka bi takwarorinsu na musulmi wajen gudanar da atisayen, ya ce sun yi hakan ne domin karfafa zamantakewa da hakuri da juna.

Rahoton da muke samu ya ce, tare suka share filin tare da kawar da sharar da ke kewayen harabar filin idin.

Kara karanta wannan

Cocin ECWA ta karyata zargin da ake mata na tilastawa Almajirai shiga addinin Krista

Yadda kiristoci suka halarci aikin share masallacin idi a Kaduna
Duk daya muke: Kiristoci sun taya Musulmai share filin Sallar Idi a Kaduna | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bitrus ya ce an kwashe kwanaki biyu ana atisayen, inji rahoton Daily Trust.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Manufar wannan hobbasa

A cewarsa:

“Mun zo nan ne don tallafa wa ’yan’uwanmu wajen yanke ciyayi da kuma share dattin da ke cikin masallacin da kewaye, da nufin wanzar da zaman lafiya da hadin kai.
“Atisayen wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu (Asabar da Lahadi) ya baiwa Kiristoci da Musulmi da dama damar tattaunawa, sada zumunci da kuma tattaunawa kan ingantattun hanyoyin da za a bi wajen inganta juriyar addini da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.
"Muna fatan za mu ci gaba da yin hakan a kowace shekara don inganta juriyar addini a yankin."

Da yake mayar da martani, Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), reshen karamar hukumar Kachia, Malam Ibrahim Tasiu, ya bayyana jin dadinsa kan yadda mabiya addinin kirista suka fito a lokacin aikin.

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

Ya bayyana cewa, matasan kiristoci sun isa filin Idin ne domin taya aiki kafin ma zuwan wasu Musulmai.

Ya yaba da wannan matakin, inda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin yankin Kudancin Kaduna, wanda ya sha fuskantar rikicin kabilanci da addini.

Ibrahim ya yi kira ga Musulmi da Kirista da su zauna lafiya da juna.

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

A wani labarin na daban, wani labari mara dadi ya zo mana cewa ‘yan bindiga sun bude wuta ga wasu Bayin Allah da suke shirin zuwa sauke faralin aikin hajji a kasa mai tsarki.

Jaridar 21st Century Chronicle ta rahoto cewa wannan lamari ya auku a ranar Litinin, a lokacin da maniyyatan suke hanyarsu ta zuwa filin tashin jirgin sama.

A safiyar Talatar nan, 21 ga watan Yuni 2022 ake sa ran cewa maniyyatan jihar Sokoto za su tashi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.