Hijabi: Lauya Ya Tafi Kotu Da Kayan Fasto Kwanaki Bayan Wani Ya Je Kotu Da Kayan Bokaye

Hijabi: Lauya Ya Tafi Kotu Da Kayan Fasto Kwanaki Bayan Wani Ya Je Kotu Da Kayan Bokaye

  • Ogbachalu Goshen, wani lauya a Jihar Anambra shima ya tafi kotu sanye da kaya irin ta rabaran fada domin ya kare wani
  • Amma da isarsa kotun, alkalin kotun ya kallubalence shi kan tufafin da yasa ya kuma ki yarda ya tsaya gaban kotun ya kare wanda ake zargin
  • Goshen, a bangarensa ya dage cewa shi dama fasto ne don haka ba laifi bane idan ya taho kotu da kayan tunda kotun koli ta halasta wa musulmi zuwa makarantu da hijabi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Anambra - Wani lauya, Ogbachalu Goshen, a ranar Alhamis ya bayyana a Kotun Majistare ta Okpoko a karamar hukumar Ogbaru kusa da Onitsha sanya da kayan raban fada.

Sai, dai an kawo karshen shari'ar a kotun cikin gaggawa, CB Mbaegbu, ya ki amincewa da shigar lauyan, ya kara da cewa ba zai yiwu ya zo kotu da wannan tufafin ya kare wani ba, The Punch ta rahato.

Kara karanta wannan

An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

Ogbachalu Goshen.
Hijabi: Lauya Ya Tafi Kotu Da Kayan Fasto Kwanaki Bayan Wani Ya Je Kotu Da Kayan Bokaye. @saharareporters.
Asali: Twitter

Goshen, a bangarensa, ya ki amincewa da alkalin kotun, ya ambaci hukuncin kotun koli da ta bawa dalibai mata damar saka hijabi a makarantun gwamnati.

Ya kuma ce yana da ikon yin hakan, yana mai cewa alkalin kotun ya danne masa hakkin da sashi na 38 na kundin tsarin mulki na 1999 na Najeriya ta bashi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kawo karshen zaman kotun bayan bangarorin biyu sun gaza cimma matsaya.

Abin da Goshen ya fada wa yan jarida

Da ya ke magana da manema labarai, Goshen ya ce bai saba doka ba duba da cewa kotun kolin Najeriya ta bada ikon saka hijabi a makarantun gwamnati da wasu hukumomin.

Lauyan ya ce kotun ba bashi amsa kan abin da za ta yi idan lauya mace musulma ta shigo kotun da hijabi.

Ya cigaba da cewa shi fasto ne don haka a kyalle shi ya sanya tufafin addininsa tunda kotun kolin ta bada daman saka hijabi.

Kara karanta wannan

2nd Class: Yadda dan fursuna ya gwama zaman kaso da karatun jami'a, kuma ya ba da mamaki

Da aka tambaye shi ko hukuncin kotun kolin ta dace, ya yanzu dole a yi biyaya tunda shine doka.

Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Sake Zuwa Kotu Da Kayan 'Bokaye'

A wani rahoton, lauya mai kare hakkin bil adama, Malcolm Omirhobo, ya bayyana gaban alkali a babban kotun tarayya da ke Legas a ranar Litinin sanye da tufafi irin na gargajiya.

Mr Omirhobo ya daura mayafi mai launin ja a kugunsa, sarkuna na gargajiya a wuyansa da kuma tufafin lauya.

Ya bayyana da irin wannan shigar a kotun koli a makon da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel