Hajji 2022: Wani maniyyyaci ɗan Najeriya ya maida makudan kuɗin da ya tsinta a Madina
- Halin kirki a ko da yaushe abun yabo ne, wani maniyyaci ɗan jihar Sokoto ya yi abun a yaba masa yayin da tsinci jaka ɗauke da kudi a Madina
- Mutumin mai suna, Arzika Bakaya, ya tsinci ƙaramar jaka ɗauke da kuɗi amma be wata-wata ba ya kaiwa jami'ai don a maida wa mai ita
- Jakar wacce mallakin wani Alhaji ne shi kuma daga jihar Kaduna, ta koma hannun me ita bayan bin matakai
Wani maniyyaci ɗan asalin jihar Sokoto ya maida yar ƙaramar jaka da ya tsinta ɗauke da dalar Amurka 700 kwatankwacin N70,000 a kuɗin Najeriya da Riyal hudu ga mai ita a Madina.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jakar ta wani maniyyaci ce kuma ɗan Najeirya da ya fito daga jihar Kaduna.
Mutumin da ya nuna halin kirki mai suna, Arzika Bakaya, ya tsinci jakar ne a kan matattakalar hawa bene da ke Otal ɗin da aka sauki Alhazan jihohin Najeriya.
Alhajin ya shaida wa hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa ko kaɗan bai yi dana sanin maida jakar da kuɗin ga mai ita na haƙiƙa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mafi ƙarancin alawus ɗin tafiya, BTA, da aka ware wa maniyyata kowanen su shi ne dala 850 yayin aikin Hajjin bana 2022/1443.
Alhaji Bakaya ya ce bayan ya tsinci jakar ya ɗauke ta zuwa ofishin hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON kuma shugaban hukumar na Madinah, Ibrahim Mahmud ya karɓa.
Maniyyacin ya ce:
"Lokacin wayar mana da kai kan aikin Hajji, Malaman mu sun faɗa mana cewa mutum ba zai tsinci kuɗi ya rike ba a Saudiya, Duk abinda ka tsinta ka maida ko doka zata kamo ka."
Sabon rikici ya ɓarke a PDP, Babban Jigo ya yi watsi da Atiku, yace wajibi mulki ya koma kudu a 2023
"Saboda haka da na ga jakar sai na ɗauke ta zuwa wurin wani jami'in hukumar jin daɗin Alhazai ta Sokoto. Sai a nan ne nagane ashe jakar na ɗauke da kuɗi, cikin sa'a tana ɗauke da lambar waya da Fasfon wani ɗan Kaduna."
Yadda aka maida wa me jakar kuɗinsa
Mahmud ya godewa Bakaya da kuma alƙawarin maida jakar ga jami'an hukumar jin daɗin Alhazan jihar Kaduna domin damƙa wa ainihin me ita.
"Ina shawartan maniyyata su ƙara kula da kuɗaɗen su da takardun su yayin da suke ƙasa mai tsarki. Damuwar da mutum zai shiga idan ya rasa kuɗinsa tana da yawa."
Yayin mika kudin, an yi addu'ar fatan Alheri ga maniyyacin da ya tsinta kuma ya mayar da kuɗin, jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya.
A wani labarin kuma Wata Hajiya yar Najeriya, Hajiya Aisha Ahmad, ta rigamu gidan gaskiya a ƙasar Saudiyya
Hajiya Aisha Ahmed ta rasu ne a Asibitin Sarki Abdul'aziz kuma tuni aka gudanar da Jana'izarta kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Nasarawa ya ce marigayyar bata da rahoton rashin lafiya kafin tafiya Saudiyya.
Asali: Legit.ng