Hajji 2022: Wata maniyyaciya yar Najeriya ta rasu a ƙasar Saudiyya

Hajji 2022: Wata maniyyaciya yar Najeriya ta rasu a ƙasar Saudiyya

  • Allah ya karbi rayuwar wata maniyyaciya yar Najeriya a ƙasa mai tsarki bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Hajiya Aisha Ahmed ta rasu ne a Asibitin Sarki Abdul'aziz kuma tuni aka gudanar da Jana'izarta kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada
  • Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Nasarawa ya ce marigayyar bata da rahoton rashin lafiya kafin tafiya Saudiyya

Wata yar Najeriya da ta yi niyyar aikin Hajjin bana 2022, Hajiya Aisha Ahmad, ta rigamu gidan gaskiya sanadin rashin lafiya a Saudiyya ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta tabbatar a rahotonta.

Aisha Ahmad, daga ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, ta rasu ne bayan kamuwa da gajeruwar rashin lafiya, a cewar Alhaji Idris Al-Makura, shugabann hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Nasarawa.

Dakin Ka'aba.
Hajji 2022: Wata mahajjaciya yar Najeriya ta rasu a ƙasar Saudiyya Hoto: Dailytrust
Asali: Getty Images

Al-Makura. ya gaya wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Laraba a Makkah cewa mamaciyar ba ta da wani rahoton rashin lafiya kafin ta bar Najeriya.

Kara karanta wannan

Masha Allah: Malami Daga Kudu Ya Fassara Kur'ani Zuwa Harshen Igbo, Za A Kaddamar A Ranar Juma'a

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mamaciyar ba ta da wani rahoton rashin lafiya kafin jirgin su ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki kuma muna tare da ita a Madinah. Mahajjaciyar ta kamu da rashin lafiya kwana biyu da suke shuɗe."
"Ita ce ta farko da muka kai Asibitin hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON) daga bisani aka maida ita Asbitin Sarki Abdul-Aziz, inda anan ne rai ya yi halinsa. Tuni muka sanar da iyalanta game da rasuwar."
"Mun ɗauki Bidiyo mun tura wa iyalan mamaciyar na yadda aka bi matakai wajen tabbatar da rasuwarta zuwa lokacin da aka mata Sallar Jana'iza har sanda aka yi mata gata na ƙarshe aka rufeta."

An ga jinjirin watan Dhul-Hijjah 1443 a Saudiyya

A wani labarin kuma An sanar da ganin jinjirin watan Babbar Sallah wato Dhul Hijjah na shekarar 1443 a Saudiyya

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mataimakin gwamna ya maka majalisar dokokin jiha a Kotu kan yunkurin tsige shi

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul-Hijjah, watan babban Sallah yau Laraba 29 ga watan Dhul- Qa'adah 1443. Hakan na nufin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, zai zama ɗaya ga wata.

Ganin watan na nuni da cewa al'ummar Musulmi a Saudiyya zasu gudanar da babbar Sallah (Eid-El-Adha) ranar Asabar 9 ga watan Yuni, 2022 dai-dai da 10ga watan Dhul-Hijjah 1443.

Asali: Legit.ng

Online view pixel