Da Dumi-Ɗumi: Sanata Ekweremadu ya bayyana gaban Kotun Birtaniya

Da Dumi-Ɗumi: Sanata Ekweremadu ya bayyana gaban Kotun Birtaniya

  • Sanata Ike Ekweremadu, ya bayyana a gaban Kotun Majistire da ke Uxbridge kan tuhumar da ake masa na yanke sassan jiki
  • Mai gabatar da ƙara ya yi ikirarin cewa wanda Sanatan ya ɗakko don ya ba ɗiyarsa ƙoda bai wuce shekara 15 ba a duniya
  • Kotu ta ɗage zaman zuwa 7 ga watan Yuli don ba Antoni Janar na Birtaniya damar nazari kan inda za'a cigaba da sauraron shari'ar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya bayyana a gaban Kotun Majistire da ke a ƙasar Birtaniya kan tuhumar da ake masa na yanke sassan jiki.

Channels tv ta ruwaito cewa mai gabatar da ƙara ya yi ikirarin cewa David Ukpo, wanda ake zargin tilasta masa aka yi ya ba ɗiyar Sanatan ƙoda, bai wuce shekara 15 ba a duniya.

Kara karanta wannan

Babban Sallah: Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tafi Hutu, Ta Sanar Da Ranar Dawowa

Sanata Ike Ekweremadu.
Da Dumi-Ɗumi: Sanata Ekweremadu ya bayyana gaban Kotun Birtaniya Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai an ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 7 ga watan Yuli, 2022 domin baiwa Antoni Janar na Birtaniya, Suella Braverman, damar yanke ko za'a cigaba da sauraron karar a ƙasar ko a maida ta Najeriya.

A ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta ce zata tura tawagar wakilai su ziyarci Sanatan da matarsa a can Birtaniya. Shugaban majalisar, Ahmad Lawan ne ya yi wannan furucin bayan wani zaman sirri da mambobi a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba mambobin kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar Dattawa zasu tafi Birtaniya.

Lawan ya ce:

"Akwai tawagar da zasu tafi Landan domin su gana da Sanata Ike Ekweremadu da matarsa. Tawagar daga cikin mambobin kwamitin harkokin waje na majalisar zasu tafi Landan kan lamarin nan da kwana biyu."
"Ina rokon duk wata hukumar gwamnatin tarayya da zata iya shiga har gaskiya ta yi halinta, ta taimaka ta bada gudummuwarta."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Hayan Lauyoyi Da Za Kare Ekweremadu Da Matarsa

FG ta haɗa tawagar Lauyoyi

Lawan ya ƙara da cewa Ofishin jakadancin Najeriya ya ɗauki hayar wasu kwararrun lauyoyi a Birtaniya domin su kare Sanata Ekweremadu.

"Na tattauna da Jakadan Najeriya a ƙasar Birtaniya, Alhaji Isola Sarafa, wanda ya yi kokari sosai game da lamarin takwaran mu, kuma ya samu damar haɗa tawagar da zasu je Kotun Uxbridge, inda aka gurfanar da Ekweremadu."

A wani labarin kuma Mataimakin gwamna ya maka majalisar dokokin jiha a Kotu kan yunkurin tsige shi

Mataima kin gwamnan jihar Oyo ya nufi babbar Kotun jiha da rokon ta dakatar da majalisar dok o kin jihar daga batun tsige shi.

Majalisar ta fara shirin tsige shi daga muƙaminsa ne bayan sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, mambobi 24 cikin 34 suka amince da korafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262