An kuma: Yan bindiga sun sake kai sabon hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace mutane
- Wasu miyagun yan fashin daji sun sace dandazon mutane a ƙauyen Sabon Gero, ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna
- Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigan sun ƙutsa har cikin gidaje sun kwashi mutane bayan kashe jami'an tsaro yan sa'kai biyu
- Kakakin rundunar yan sanda Kaduna ya ce ba shi da masaniya amma zai bincika ya ji ainihin abinda ya faru
Kaduna - 'Yan bindiga sun sake kai hari ƙauyen Sabon Gero da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, sun kashe jami'an tsaron Joint Task Force (JTF) guda biyu.
Yayin harin, yan ta'addan sun kuma sace mutane maza da mata da suka haɗa da mai ba da magunguna da matarsa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai wasu bayanai sun nuna cewa mutum Shida daga cikin waɗan da maharan suka sace sun yi nasarar kuttowa daga hannun yan bindigan.
A cewar wani shaidan gani da ido wanda ya nemi a ɓoye sunansa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutumin ya ce:
"Wasu daga cikin mu ba su yi bacci ba suna harkokin dake kansu lokacin da muka fara jiyo karar harbe-harben bindiga. Yan bindigan sun kutsa gidajen mutane suka tasa su, suka haɗa da wasu masu kokarin guduwa."
Wata majiyar ya bayyana cewa, "Na gano cewa an ƙashe dakarun JTF mutum biyu a harin yayin da suka yi kokarin hana yan bindigan sace mutane."
Shin hukumomi sun san da aukuwar lamarin?
Yayin da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai kira daga baya amma ba shi da masaniya a dai-dai lokacin da muke haɗa wannan rahoton.
Wannan harin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan mahara sun sace mutum Bakwai daga ƙauyen Keke A da Keke B a yankin cikin su har matar wani Soja.
A wani labarin kuma Sojoji sun yi wa yan ta'addan Boko Haram kwantan bauna, sun tura su lahira, sun kwato makamai
A cigaban da kokarin dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Sojin Operation Haɗin Kai sun ƙara samun nasara kan Boko Haram.
Sojoji tare da haɗin guiwa r jami'an CJTF sun yi wa wata tawagar mayaƙan Boko Haram kwantan ɓauna, sun halaka uku.
Asali: Legit.ng