Kano: Karancin Na'urorin Tace Jini Yana Barazana ga Rayukan Masu Ciwon Koda

Kano: Karancin Na'urorin Tace Jini Yana Barazana ga Rayukan Masu Ciwon Koda

  • A halin yanzu, jihar Kano na fuskantar barazana a bangaren lafiyar jama'a sakamakon barkewar cutar koda a fadin jihar
  • Bincike ya bayyana yadda ma'aikatan lafiya a asibitocin jihar ke korafin karancin na'urorin tacwe jini ga masu cutar koda
  • Sai dai, kwararru sun bayyana yadda amfani da tsirarun kayan aikin ya zama babban ci baya ga jihar baki daya

Kano - Rahotanni na cigaba da tabbatar da yadda harkar kiwon lafiyar jihar Kano ke tsaka mai wuya, bayan cigaba da samun masu fama da cutar koda a jihar.

Kamar yadda PRNigeria ta fitar da rahoto a ranar Lahadi 26 ga watan Yuni, an gano yadda matsanancin ciwon koda (CKD) ke cigaba da kamari a Kano.

Masu cutar koda a Kano
Kano: Karancin Na'urorin Tace Jini Yana Barazana ga Rayukan Masu Ciwon Koda. Hoto daga Guardian.ng
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta tattaro yadda a kalla masu fama da cutar koda 200 ke dogaro da injina 12 na tace jini a manyan asibitoci biyu a Kano, asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da asibitin kwararru na Abdullahi Wase.

Bincike ya tabbatar da yadda kimanin marasa lafiya 160 da ke fama da cutukan da suka shafi koda ke ziyartar asibitin kwararru na Abdullahi Wase duk karshen mako.

Haka zalika, akwai a kalla marasa lafiya 15 da ke zuwa gwajin cutar a asibitin kwararrun duk karshen mako.

Yayin da asibitin koyarwa na Aminu Kano ke tarbar marasa lafiya 70 duk karshen mako don tace jini sakamakon cutar koda. Sai dai a mako guda ake kula da a kalla marasa lafiya 40 ko fiye yayin da saura ke zaman jira.

Abun takaici shi yadda aka gano cewa da yawan sauran injinan tace jinin na masu cutar kodar a manyan cibiyoyin magance cutar a Kano basa aiki.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Har ila yau, an gano yadda a asibitin koyarwa na Aminu Kano, takwas ne kacal daga cikin injinan ke aiki a yanzu, marasa lafiyar da ke fama da cutar koda na daukar tsawon awa 10 suna jira kafin layi yazo kansu.

Yayin martani ga lamarin, Farfesa Aliyu Abdu, wanda babban likitan koda ne kuma shugaban sashin kula da koda a asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya ce yana da matukar wahala iya aiki da tsirarun injinan tace jini tare da marasa lafiya masu dumbin yawa suna jira.

A cewarsa: "A da muna da injinan tace jin na masu cutar koda guda 20, amma saboda karancin hannun jari a harkar lafiya a yanzu bama da fiye da injina biyar lafiyayyu.
"Yana da matukar wahala jure hakan. Za ka ga marasa lafiya na zaman jiran wajan awanni 10 zuwa 15 don a lura da matsalar kodarsu saboda idan ka dora mara lafiya kan Injin kula da cutar, dole mara lafiyan ya dauki tsawon awanni 4 a ciki, sannan kana bukatar wata awa daya don gyara gami da kashe kwayoyin cutar injin din kafin wani mara lafiyan ya samu damar shiga.

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

"Saboda haka, idan za ka gani a rana, ba za ka iya daukar fiye da marasa lafiya uku ba a injin daya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng