Yanzu-Yanzu: Wata mummunar gobara ta tashi a wani katafaren ginin Legas

Yanzu-Yanzu: Wata mummunar gobara ta tashi a wani katafaren ginin Legas

  • Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Legas (LASEMA) ta sake kai dauki tare da ceto wani gini da gobara ta tashi a titin Broad, CMS, Legas
  • Rahotanni sun bayyana cewa, tawagar jami’an agajin gaggawa ta LASEMA ta isa wurin da lamarin ya faru bayan samar dasu lamarin
  • LASEMA ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba, amma gobarar ta lalata kadarori da yawa da ba a sana adadinsu ba

Jihar Legas - An samu tashin wata gobara a wani gini da ke lamba 118 a Broad Street, CMS a babban birnin jihar Legas Legas, Tribune Online ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ya fitar, hukumar ta gaggauta daukar mataki ga lamarin wanda aka tura wa LASEMA ta lambar wayar gaggawa ta 112 a safiyar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Gobara ta kama a wani katafaren ginin jihar Legas
Yanzu-Yanzu: Wata mummunar gobara ta tashi a wani shararren ginin Legas | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

The Guardian ta rahoto yankin sanarwar ma cewa:

“Lokacin da aka isa wurin da lamarin ya faru, an gano cewa wani daki na ajiyar kaya da ake ajiye takalma ya kone kurmus.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Gobarar ta tashi ne a sakamakon tartsatsin wuta a lokacin da aka dawo da wutar lantarki.
“Abin farin ciki ba a samu asarar rai ba a lamarin. Tawagar hukumar da ke aikin gaggawa tare da kashe gobarar LRU da hukumar kashe gobara ta jihar Legas da kuma hukumar kashe gobara ta tarayya sun ba da agaji a wurin da lamarin ya faru tare da hada gwiwa don kashe gobarar. Ana ci gaba da gudanar da aikin.”

Kaduna: Gobara ta tashi a kwalejin ilimi ta Zaria, ta barnata kwamfutoci 100

A wani labarin na daban, sama da kwamfutoci 100 ne suka lalace a wata gobara da ta tashi a Sashen Kwamfuta na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zaria a Jihar Kaduna, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na

Jami’an kashe gobara sun dauki tsawon lokaci suna gwabzawa domin shawo kan gobarar da ta tashi da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar lokacin da ma’aikata ba sa wurin aiki.

Shugaban kwalejin, Dakta Suleiman Balarabe, ya ce gobarar ta tashi ne daga wata na'urar hana katsewar wutar lantarki (UPS).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.