Hadimin alkali: Babban dalilin da yasa shugaban alkalan Najeriya ya yi murabus
- Wani hadimin shugaban alkalan Najeriya, Justis Ibrahim Muhammad Tanko ya tabbatar da murabus din uban gidansa
- Ahuraka Yusuf Isah ya tabbatar da ci gaban ne ta wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni
- Kwatsam, aka samu labari shugaban alkalan Najeriya ya ajiye aikinsa, lamarin ya sanya wa 'yan Najeriya alamomin tambaya da yawa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Babban alkalin Najeriya, mai shari'a Ibrahim Muhammad ya yi murabus daga kujerarsa domin ya samu damar kula da lafiyarsa.
Hadiminsa, Ahuraka Yusuf Isah ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya saki dazun nan.
Koda dai da farko Isah ya karyata batun samun masaniya kan ci gaban, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da babban alkalin kotun koli na gaba, Justis Olukayoddde Ariwoola.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Justis Muhammed ya isa ofishinsa a safiyar yau Litinin, ba tare da tawagar motoci da na tsaro da suka saba take masa baya ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya dan tsaya a takaice sannan ya tafi, amma har zuwa lokacin bai dawo ba, inji wani jami’i.
Hakazalika ba a ya Justis Muhammad ba a wajen taron karawa juna sani na alkalai da aka gudanar ba a yau, wanda majalisar alkalai ta kasa ta shirya kuma ake sanya ran shine zai bude shi.
An shiga ruɗani kan batun Murabus ɗin CJN Tanko Muhammad
A baya mun ji cewa an shiga ruɗani da rashin makama kan harkokin sashin shari'a masu alaƙa da ofishin shugaban alƙalan Najeriya (CJN), kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Yayin da rahotanni ke yawo cewa Alkalin Alkalai na ƙasa, CJN Tanko Muhammad, ya miƙa takardar murabus daga kan mukaminsa, hukumomin shari'a sun ƙi cewa komai kan lamarin.
Har yanzu, Kotun Ƙoli, hukumar kula da harkokin shari'a ta tarayya (FJSC) da hukumar (NJC) sun yi gum sun ƙi tabbatar da rahoto ko kuma akasin haka.
Asali: Legit.ng