A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya umarci hukumomin tsaron jihar da su maida hankali wajen tsare rayukan mazauna kauyuka daga harin masu garkuwa da mutane
  • Ya fadi hakan ne yayin da yaje yi wa mutanen Toro jaje tare da yin ta'aziyya ga iyayen yarinyar da makwabci ya sace gami da halaka ta
  • Haka zalika, gwamnan ya lashi takobin kawo karshen ta'addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane, inda ya ce shi zai jagoranci mutane a matsayinsa na kauran Bauchi

Toro, Bauchi - Bala Muhammad, gwamnan jihar Bauchi, ya bukaci jami'an tsaron jihar da su samar da wani mataki wajen tsare kauyuka daga 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Gwamnan ya bada umarnin ne yayin da ya je ta'aziyya yankin Narabi na Sabon Gari cikin karamar hukumar Toro a jihar, inda ake zargin makwabci da yin garkuwa gami da halaka wata Khadija Abdullahi, yarinya mai shekaru biyar.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa ba Zamu Saki Nyame da Dariye ba Duk da Anyi Musu Rangwame, Hukumar Gidajen Gyaran Hali

Gwaman Bala Mohammed, Kauran Bauchi
A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

TheCable ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bukaci Umar Sanda, kwamishinan'yan sanda, da ya canza shugaban 'yan sandan yankuna na fadin kananan hukumomi 20 don magance matsalar ta'addanci da fashi da makami da garkuwa ada mutane.

"Mun zo nan ne don mu yi jaje ga mutanen Toro bisa yadda 'yan bindiga ke cin karensu ba babbaka inda kusan lamurran ta'addanci takwas suka faru a jere a yankin Narabi. Hakan ba abun amincewa bane," a cewar Muhammad.
"Wanda ya aikata mummunan aikin ya shiga hannu kuma an gurfanar da shi gaban kotu. Zamu bibiyi lamarin tare da mayar da hankali a kai.
"Ya kamata shugabannin anguwanni su kara sa ido saboda rashin tsaro yanzu ya zama ruwan dare. Muna da mutane da ke shigowa cikin Toro da Alkaleri saboda girman kananan hukumomin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindigu da Makaman Yakar 'Yan Ta'adda

"Za mu tabbatar mun sa idanuwanmu da kafafun mu a kasa, saboda haka muna rokonku da ku bamu hadin kai.
"Babu wanda zai baku tsaro sai kun fara bawa kawunanku. Ku zama masu jajircewa kada ku ji tsoro.
"Mu ba tarin ragwaye bane. A matsayina na Kauran Bauchi, jagoran sadaukan dukkan masarautu, a shirye nake da in jagorance ku.
"Saboda haka ina rokonku, duk abun da muke da shi a ajiye ku fito da shi. Dole mu tunkari wadannan hatsabiban, shu'uman kuma kangararrun sannan dole ne su kawo karshensu."

Ta bangaren sa, Sanda ya tabbatar da kama wasu daga cikin masu alhaki a ta'addancin, duk da wanda ake zargi da halaka yarinyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng