Gwamna Ya Bai wa 'Yan Bindiga Wa'adin Kwanaki 10 Su Mika Kansu Ko Ya Dauka Mataki
- Yayin da jihar Imo ke sa ran karbar bakuncin Buhari, Gwamna Hope Uzodimma ya bawa 'yan bindigan da ke cin karensu ba babbaka wa'adin kwanaki 10 su tuba
- A cewar Uzodimma, wajibi ne 'yan bindigan su mika makamansu da kawunansu cikin kwanakin 10 tare da alkawarin ba za a musu komai, kafin cikar wa'adin
- Ya bayyana yadda ake shirya bikin zagayowar ranar sojoji daga 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli wanda a kalla jami'an tsaron sojoji 10,000 zasu samu damar halarta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Imo - Yayin da ake jiran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Imo a ranar 12 ga watan Yuli, Gwamna Hope Uzodimma ya bawa 'yan bindiga da ke aiwatar da lamurran ta'addanci a jihar kwana 10 da su aje makamansu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Uzodimma ya shawarcesu da su bar dajikan jihar kuma su kawo kawunansu da makamansu ga shugabannin gargajiya don a masu rangwame.
Yayin zantawa da manema labarai a Owerri, Uzodimma ya bayyana yadda jihar zata gudanar da shagalin zagayowar ranar sojoji daga 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli kuma a kalla jami'an soji 10,000 daga sansanin sojin kasa, na ruwa, na sama da 'yan sanda zasu samu damar halartar taron.
Ya ce shugaban kasa, wanda ake sa ran ya sanar da bikin zagayowar ranar sojoji ya sa 12 da 13 ga watan Yuli a matsayin lokutan kaddamar da titinan Owerri-Orlu da Owerri-Okigwe tare da ranar taya alhini ga tarwatsa kungiyar kwana-kwana ta Owerri-Mbaise-Umuahia da titinan Orlu-Akokwa da bikin kafa kungiyar ta Imo International Conference Centre a Owerri.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, "A yanzu jihar tafi maida hankali ga shirin wajen son ganin ta sheke duk 'yan bindiga, kuma kafin a samu damar yin hakan, ana sa ran tanadar kayan aiki da jami'an Ebube-Agu tare da hadin guiwar hukumomin tsaron jihar da duk wata hanya ruwa da kafar da 'yan bindiga suke duk da masu satar man fetur.
"Ana kan gyaran duk wasu hanyoyin ruwa tare da kawo duka wasu kayayyakin yaki a sansanin sojin ruwan Oguta."
Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindigu da Makaman Yakar 'Yan Ta'adda
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga mazauna jihar da su dauka makamai tare da bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga.
A yayin da korafi kan tabarbarewar tsaro ta yawaita a jihar, hukumomin Zamfara sun umarci kwamishinan 'yan sandan jihar sa ya bada lasisin rike bindigu ga wadanda suka dace su rike a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin tace a shirye take da ta tabbatar da jama'a sun samu makamai ballantana manoma, domin bai wa kansu kariya.
Asali: Legit.ng