Gwamna Uzodinma ya ba yan bindiga kwanaki 10 su aje makamansu ko su funkanci ruwan wuta

Gwamna Uzodinma ya ba yan bindiga kwanaki 10 su aje makamansu ko su funkanci ruwan wuta

  • Gwamnan jihar Imo ya ba yan bindiga wa'adin kwanaki 10 su miƙa makamansu ko su fuskanci ruwan wuta ba kakkautawa
  • Yayin da gwamnan ke shirin karɓan bakuncin shugaban ƙasa Buhari, ya shawarci yan ta'adda su gaggauta barin dazukan jihar Imo
  • Hope Uzodinma, ya ce jiharsa zata karɓi bakuncin bikin shekara-shekara na hukumomin tsaro wanda za'a fara daga 30 ga watan Yuni

Imo - Gabanin ziyarar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zuwa Imo ranar 12 ga watan Yuli, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya ba 'yan bindiga da suka hana zaman lafiya wa'adin kwanaki 10 su miƙa wuya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Uzodinma ya shawarci 'yan bindigan su bar dazukan jihar kuma su miƙa wuya tare da damƙa makamansu ga Sarakunan gargajiya don a yafe musu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Koli ta yi fatali da karar da Shugaba Buhari, Malami suka shigar kan dokar zaɓe

Da yake jawabi ga manema labarai a Owerri, Gwamnan ya ce jihar Imo zata karɓi bakuncin bikin shekara-shekara na sojojin Najeriya daga 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Gwamna Uzodinma ya ba yan bindiga kwanaki 10 su aje makamansu ko su funkanci ruwan wuta Hoto: Hope Uzodinma/facebook
Asali: Facebook

A cewarsa, akalla dakarun tsaro 10,000 daga hukumar sojojin ƙasa, na sama da na ruwa da kuma yan sanda, zasu halarci bikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ƙara da cewa jihar Imo zata karɓi sabbin kayan aikin jami'an tsaro, waɗan da za'a yi amfani da su wajen share ƴan bindiga a wuraren da suke ɓuya cikin dazuka daban-daban a faɗin jihar.

Vanguard ta rahoto Uzodinma ya ce:

"Jihar mu ta shirya fiye da baya domin kakkaɓe baki ɗaya 'yan bindiga, don cimma haka zamu tanadi sabbin kayan aiki kuma zamu ɗauki ƙarin dakarun Ebube-Agu da zasu yi aiki tare da hukumomin tsaro."
"Zasu tsaftace dukkan hanyoyin ruwa da kuma yan bindiga haɗi da ɓarayin mai. Duk hanyoyin ruwan mu zasu kasance cikin kula da zaran kayan aiki sun isa ga sojojin ruwa a sansanin su na Oguta."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa a babban ɗan sanda a Nasarawa, sun bukaci Miliyoyi

Ayyukan da Buhari zai yi yayin ziyara a Imo

Uzodinma ya ce shugaban kasa, wanda ake tsammanin zai buɗe bikin ranar ta Sojoji, ya zaɓi ranakun 12 da 13 ga watan Yulin domin buɗe wasu ayyuka.

A cewar gwamnan Buhari zai buɗe hanyoyin Owerri-Orlu da Owerri-Okigwe, kana ya kaddamar da fara aikin hanyar Owerri-Mbaise-Umuahia (daga hukumar kashe gobara) da hanyar Orlu-Akokwa.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun karya yarjejeniyar zaman lafiya, sun sheke mutan kauyen Neja

Wannan na zuwa ne a karshen makon nan yayin da jama'ar yankin ke kokarin fara ayyukansu na gona.

Wani mazaunin yankin ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin ya faru da kuma irin cin amanan da suka fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262