Za a rina: 'Yan bindiga sun karya yarjejeniyar zaman lafiya, sun sheke mutan kauyen Neja

Za a rina: 'Yan bindiga sun karya yarjejeniyar zaman lafiya, sun sheke mutan kauyen Neja

  • Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya, 'yan bindiga sun saba alkawari sun hallaka mutane a jihar Neja
  • Wannan na zuwa ne a karshen makon nan yayin da jama'ar yankin ke kokarin fara ayyukansu na gona
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin ya faru da kuma irin cin amanan da suka fuskanta

Kombo, jihar Neja - Rahotanni sun ce an kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu da dama daga yammacin ranar Asabar zuwa safiyar Lahadi a kauyen Kombo da ke gundumar Kusherki a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

An kuma ce mutum daya ya samu munanan raunuka kuma yana karbar magani da kulawar asibiti, Daily Trust ta ruwaito.

Wani rahoto da jaridar Punch ta fitar a baya ya bayyana cewa, 'yan bindiga da mazauna yankunan jihar Neja sun yi yarjejeniyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

'Yan bindiga sun karya alkawari, sun hallaka jama'a a Neja
Tir: 'Yan bindiga sun karya yarjajeiyar zaman lafiya, sun sheke mutan kauyen jihar Neja | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Harin dai ya zo ne kasa da mako guda da ‘yan bindigan suka shiga yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomin yankunan tare da yi musu alkawarin za a zauna lafiya cikin lumana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mazaunin yankin da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun yi matukar bakin ciki da harin na baya-bayan nan.

Ya ce duk da cewa gungun da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da su sun musanta cewa su suka kai harin na baya-bayan nan, amma ba su da kwarin gwiwar imani da yarjejeniyar zaman lafiya.

Ya koka da cewa harin ya zo ne a lokacin da ake shirye-shiryen komawa gida domin fara ayyukan noma.

Yadda lamarin ya faru dalla-dalla

Ya shaidawa Daily Trust cewa:

“Mun yi bakin ciki kuma mun ji zafi. Dukanmu mun gudu daga gidajenmu; yau ma babu wanda ya je gona.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

"Da yammacin ranar Asabar, sun yi garkuwa da mutane da dama a cikin al'ummomi daban-daban. Sun dawo cikin dare sun kashe mutum uku tare da raunata mutum daya a garin Kombo da ke kusa da unguwar Zara mai tazarar kilomita kadan da Birnin Gwari a jihar Kaduna.
“Damuwarmu a yanzu ita ce yadda aka yi watsi da mu kamar ba ’yan Najeriya ba. Duk wadannan hare-hare ba mu taba ganin jami’an tsaro ko da suna sintiri a cikin al’ummarmu ba.
“Duk da haka, ba mu gane ma'anar yarjejeniyar zaman lafiyar da muka kulla da wadannan ‘yan bindigar ba, domin ko bayan tattaunawa kan yarjejeniyar, sun ki sakin sauran mutanen da suka yi garkuwa da su a baya. Kuma an sake kai mana hari.
“Mun yi tunanin bayan yarjejeniyar zaman lafiyar, za mu zauna lafiya kuma mutanenmu suna komawa gida suna gudanar da ayyukan noma.
“Amma gungun da muka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da su sun musanta alhakin kai sabon harin. Wani abin mamaki sai su ('yan bindigan) suka ce mana za su sanar da wasu gungu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da su. Hakan ne ma ya sa suka bukaci a ba su kudi don sayen goro domin rabawa ga sauran gungun.”

Kara karanta wannan

Al’ummar jihar Neja sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya da yan bindiga

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ci tura, saboda ba a iya samun layin wayarsa.

Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

A wani labarin, kafar labarai ta Channels ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda shida a fagagen ayyukan ta daban-daban.

Mahukuntan sojojin sun kuma ce sojojin sun kama wasu da ke hada kai da maharan, ciki har da wani fitaccen dillalin bindigu da kuma samar da kayan aikin Boko Haram.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya fitar, hedkwatar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel