Wata Sabuwa: Na Tsunduma Cikin Kogin Soyayya Da 'Katanga', In Ji Matar Da Ta 'Auri' Husumiyar Eiffel

Wata Sabuwa: Na Tsunduma Cikin Kogin Soyayya Da 'Katanga', In Ji Matar Da Ta 'Auri' Husumiyar Eiffel

  • Wata baamurkiya mai suna Eric LaBrie wacce ta yi fice saboda sha'awar abubuwa marasa rai ta ce tana sha'awar wani katanga
  • LaBrie, wacce ta 'auri' Husumiyar Eiffel tun a shekarar 2007 ta ce tana yi wa katangar sha'awa irin wanda masoya ke yi wa juna
  • A wani bidiyo da ta wallafa kuma ya bazu a dandalin sada zumunta, LaBrie ta ce tabbas tana son ta zurfafa soyayyanta da katangar na katako

Amurka - Eric LaBrie, matar da ta yi fice saboda soyayya da abubuwa marasa rai ta ce tana sha'awar Husumiyar Eiffel, irin sha'awa da ake yi wa mutum, rahoton The Cable.

A wani bidiyo da ya bazu, an hangi LaBrie, wacce yar Amurka ce mai gasar harbin kwari da baka kuma mai kare hakkin masu kaunar abubuwa marasa rai, tana zaune kan wani katanga na katako tana mai nuna sha'awarta ga katangar.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Ce A Bawa Abubakar Masauki a Gidan Yari Saboda Dage Wa Wata Gyale Ba Da Izininta Ba

Eric LaBrie.
Ina Sha'awar 'Katanga' In Ji Matar Da Ta 'Auri' Husumiyar Eiffel. @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

LaBrie tana kiran kanta 'objectum sexual' - ma'ana wanda ke yi wa abubuwa marasa rai sha'awa irin ta tsakanin mace da namiji.

"Ban taba tsammanin zan ga katanga irin wannan a nan ba. Shi (katangar) yana da matukar kyawun suffa. Irin wannan sufar na ke so sosai. Abin sha'awa," in ji ta.

A faifan bidiyon, matar ta ce katangar ya 'burge' ta matuka. LaBrie ta kara da cewa ta kan yi saurin sha'awar katanga saboda 'babu abin kushewa a sifarsu.'

"Katanga abin hatsari ne a gare ni domin babu abin kushe wa a sifarsu," ta kara da cewa.
"Gaskiya, ina matukar jin sha'awarsa a yanzu.
"Tabbas ina sha'awar wannan katangar kuma zan so mu zurfafa soyayyar mu."

Bidiyon, wanda an kalle shi fiye da miliyan daya a TikTok, yana cigaba da daukan hankulan mutane a dandalin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

LaBrie ta yi fice ne a shekarar 2007 saboda 'auren' Husumiyar Eiffel da ke Birnin Paris a Faransa inda aka yi biki.

Ku Dena Yi Wa Mazajenku Rowa Yayin Kwanciyar Aure, Likita Ya Faɗa Wa Mata Illar Yin Hakan

A wani rahoton, Eric Okunna, wani kwararren likitan mata, ya ce alfano da ke tattare da kwanciyar aure mai nagarta ba zai misaltu ba, rahon The Cable.

A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, likitan ya tambayi ra'ayoyin wasu mazauna Awka, Jihar Anambra, kan batutuwan da suka shafi rayuwar aure musamman kwanciyar aure.

Ya ce wadanda suka amsa tambayoyinsa sun ce bai dace ma'aurata su rika hana juna hakkin kwanciyar aure ba musamman mata ga mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel