Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana irin namijin aikin da jami'an soji suka yi a cikin kwanakin nan
  • Daga ayyukan, rundunar ta bayyana cewa an kama wasu jiga-jigan 'yan ta'addan da suka addabi sassan kasar nan
  • Rundunar ta kuma yabawa jami'ai, inda ta nemi su ci gaba da gashi tare da ragargazar tsagerun 'yan ta'adda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kafar labarai ta Channels ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda shida a fagagen ayyukan ta daban-daban.

Mahukuntan sojojin sun kuma ce sojojin sun kama wasu da ke hada kai da maharan, ciki har da wani fitaccen dillalin bindigu da kuma samar da kayan aikin Boko Haram.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya fitar, hedkwatar tsaro.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun Sojoji Sun Kashe Wasu 'Yan Ta'adda Shida Dake Tallafawa Boko Haram | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar ta bayyana cewa, dakarun Operation Hadarin Daji sun amsa kiraye-kirayen mazauna kan barnar da ‘yan ta’adda suka yi a Rafin Dankura da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da wasu fararen hula.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Janar Onyeuko ya ce sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addan kuma a cikin haka ne sojojin suka ceto shida daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su tare da kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan.

Onyeuko ya bayyana cewa:

“Abubuwan da aka kwato sun hada da AK 47, gurneti mai girman 1x36, wayoyin salula 2 da kudi 211,915.00."

An dakile 'yan ta'adda tare da kame wasu

Hakazalika a ranar 21 ga watan Yunin 2022 a martanin da sojojin suka yi a kan ayyukan ta'addanci, sun yi tuntubar 'yan ta'addar da suka yi garkuwa da wasu a Maigora da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina tare da kashe 'yan ta'adda biyu a cikin aikin.

Janar Onyeuko ya ci gaba da bayyana cewa dakarun Operation Whirl Stroke sun kama wani kasurgumin dillalin bindiga mai suna Ardo Manu Andulrahaman Maranewo a ranar 20 ga watan Yunin 2022, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

Maranewo wanda ya kasance cikin jerin sunayen wadanda jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo an ce ya kware wajen sayar da makamai ga ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane a jihar Taraba.

Hakazalika, a ranar 20 ga watan Yuni, sojojin bataliya ta 151 na Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar CJTF da ke sintiri na tabbatar da tsaro sun ragargaji 'yan ta'adda a kan hanyar Bama-Pulka.

An kashe biyu daga cikin 'yan ta'addan, sannan an kwato bindigogi da harsasai na gida guda biyu daga hannunsu.

A wannan rana ne wani dan ta'addan Boko Haram, Malam Modu Rija ya mika wuya ga sojojin Najeriya a yankin Tashangoto. Kayayyakin da aka kwato daga hannunsa sun hada da bindiga kirar AK 47 guda daya, da gurneti mai girman 1×36, da harsashi 26 na alburusai masu girman 7.62mm.

Hakazalika, a ranar 21 ga watan Yunin 2022 sojoji sun kama wani dan Boko Haram, Malam Abacha Usman a Benishek da kuma wani mai safarar kayan aikin ta'addanci, Mallam Ibrahim Gira.

Kara karanta wannan

Ana shirin yin waje da duk wani Sojan da ba a gama yarda da imaninsa ba a Najeriya

An kama su ne a hanyar Dambua zuwa Biu duk a jihar Borno.

Janar Onyeuko ya ce, rundunar sojin ta yaba da kokarin da sojojin ke yi, ya kuma kara da cewa suna kara karfafa gwiwar su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na hedkwata na tare dasu.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya a wata jiha

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken al’ummar Isuokoma mai cin gashin kansa a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi, Eze Ambrose Ogbu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wasu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun yi awon gaba da sarkin ne a daren ranar Laraba a fadarsa da ke Isu a yankin karamar hukumar.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Abakaliki a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.