Da Ɗumi-Dumi: Kotun Koli ta yi watsi da ƙarar shugaba Buhari da Malami kan dokar zaɓe
- Kotun Koli ta yi watsi da ƙarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da Malami wacce suka shigar kan dokar zaɓe ta sashin 84(12)
- Kotu a yau Jumu'a ta yanke cewa shugaban kasa, wanda ya rattaɓa hannu kan dokar, ba shi da ikon baiwa majalisa umarni kan aikin su
- Ta ce Kotun koli ba ta hurumin shiga lamarin kuma karar cin mutunci ne ga tsarin Kotu da tsarin demokaraɗiyya
Abuja - Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, suka shigar inda suka buƙaci a share sashi na 84 (12) na sabon kundin zaɓe 2022.
Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, kwamitin Alƙalai Bakwai bisa jagorancin Mai Shari'a Musa Dattijo Mohammed, sun cimma matsaya guda cewa Buhari, kasancewar da shi aka yi dokar ya rattaɓa hannu a kai, ba zai dawo yana yaƙar wani sashi ba.
The Nation ta rahoto, Kotun bayan ta karbi bayanan majalisar tarayya da sauran waɗan da ake ƙara, ta bayyana cewa Kotun Ƙoli ba ta hurumin sauraron lamarin kuma ƙarar cin mutunci ne ga tsarin Kotu.
Da yake bayyana matsayar Kotu, Mai Shari'a Emmanuel Agim, ya ce shugaban ƙasa ya umarci bangaren masu yin doka su yi wata doka ko su canza wata farmaki ne ga tsarin Demokaraɗiyya wanda ya rarraba iko.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daily Trust ta ruwaito Agim ya ce:
"Shugaban ƙasa ba shi da ƙarfin ikon umartan majalisar tarayya ta yi wa doka garambawul ko ta share wata doka, wacce da sa hnnun sa aka yi dokar, ya saɓa wa tsarin demokaraɗiyya na raba karfin iko."
"Babu wani wurin a kudin tsarin mulkin ƙasa da ya tanadi ɓangaren masu yin doka su saurari umarnin shugaban ƙasa wajen ayyukan su."
Kotu ba zata cigaba da sauraron wannan ƙarar ba karkashin sashi na 1 (1) (a) na kundin dokokin Kotun Ƙoli."
A wani labarin kuma ko kun san Gaskiyar abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotun Landan kan zargin yanke sassan jiki
Sanata Ike Ekweremadu da matarsa sun gurfana a gaban Kotun Majirstire a Landan, kuma sun yi kokarin kare kan su kan zargin safara.
Ta bakin lauyoyin su, Gavin Irwin da Antonia Gray, sun musanta tuhumar da ake musu na safarar mutane da nufin yanke sassan jikin su.
Asali: Legit.ng