Ba Zabin Biyan Tara: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Dauri Saboda Satar Tukunyar Jar Miya Da Nama a Ibadan
- Wata kotu da ke zamanta a Ibadan ta yanke wa wani matashi Isaac Dumabara, dan shekaru 23 hukuncin daurin wata daya a gidan gyaran hali
- Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin ne ba tare da zabin biyan tara ba bayan an same shi da laifin satar tukunyar jar miya da nama zuku-zuku da darajarta ta kai N40,000
- Dan sanda mai gabatar da kara, Sikiru Ibrahim, tunda farko ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya kuma saci talabijin mai inci 42, tunkunyar gas da takalma
Ibadan - Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ibadan, a ranar Laraba ta yanke wa wani mutum dan shekara 23, Isaac Dumabara, hukuncin daurin wata daya saboda satar tukunyar jar miya da nama da kudinta ya kai N40,000 daga wurin sayar da abinci.
Alkalin kotun S.A. Adesina, wanda ya samu wanda ake zargin da laifin sata, ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na wata daya ba tare da zabin biyan tara ba, Premium Times ta rahoto.
Tunda farko, dan sanda mai shigar da kara, Sikiru Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa Mr Damubara kuma ya sace tukunyar gas, stablizer da takalma kirar adidas daga 'Pleasure Summit Restaurant' da ke Magara Road, Iyaganku, Ibadan.
Mr Ibrahim ya kuma shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya saci talabijin mai fadin inci 42 da kudinsa ya kai N200,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce laifukan sun saba wa sashi na 390(9) na kundin dokokin masu laifi na Jihar Oyo ta shekarar 2000, kamar yadda NAN ta rahoto.
A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa
A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.
Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.
Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.
Asali: Legit.ng