Daya daga cikin 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH
- Rundunar sojin Najeriya ta ceto wasu 'yan mata da suka dade a hannun tsagerun 'yan Boko Haram tun 2014
- A bayanin da daya daga cikin 'yan matan ta yi, ta ce ta ga marigayi Shekau a cikin dajin Sambisa
- Daya kuwa ta ce, bata san shi ido da ido ba, amma ta sha ganin yana ba tsagerun kwamandojinsa umarni ta kwamfuta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Shekaru takwas bayan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata 276 a makarantar Sakandaren Chibok a Borno, rundunar sojin Operation Hadin Kai ta ceto wasu karin ‘yan matan Chibok biyu a dajin Sambisa.
An ce rundunar ta ceto su ne a yankin Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno a kwanan baya. Wadanda aka kubutar din su ne Mariam Dauda da Hauwa Joseph ne tare da jariransu, Daily Trust ta ruwaito.
Bayan ceto su sun ba da labarin wahalar da suka sha na tsawon shekaru takwas a cikin dajin a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban dakin taro na Command-and-Control Center da ke Maimalari a Maiduguri ranar Talata.
Sun bayyana cewa an daura musu aure da Kwamandojin Boko Haram tsawon shekaru kuma dukkansu sun haifa musu jarirai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ci gaba da cewa sojojin Najeriya sun kashe mazajensu watanni da suka gabata.
Yayin da take amsa tambayoyin manema labarai, Mary wacce a yanzu sunanta Mariam ta ce:
“Eh na san shi, na taba ganin marigayi Abubakar Shehu."
Ta ci gaba da cewa:
“Eh, har yanzu akwai sauran ‘yan matan Chibok a dajin Sambisa. Suma sun yi aure, akalla sama da 20 suna can.”
Ta kuma ambato sunayensu daya bayan daya.
A cewarta:
“Ina da shekara 18 a lokacin da suka sace mu kuma na musulunta, ni Kirista ce amma suka musuluntar dani suka aurar da mu.
“Mun gode wa Allah da a karshe muka kubuta, mun sha wahala bayan an kashe mazajenmu, rayuwa ta kuntata a gare mu. Muna godiya ga sojojin da suka kubutar da mu.”
A nata bangaren, Hauwa ta yi ikirarin cewa ba ta taba ganin marigayi Shekau da kansa ba.
A cewarta:
"Ban taba ganinsa ido da ido ba amma ina kallonsa a kwamfutar tafi-da-gidanka yana ba da umarni ga mayakan."
Sun godewa sojojin da suka kubutar da su bayan da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su tsawon shekaru takwas.
Kokarin da soji ke yi
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Christopher Musa, ya ce an samu nasarar ne sakamakon gagarumin farmakin da sojoji suka kai a dajin Sambisa, da tsaunin Mandara, da yankin tafkin Chadi.
Ya kuma lura cewa an ceto ‘yan matan ne a Sambisa yayin da yake ba da tabbacin cewa ba za su huta ba har sai sauran wadanda aka sace sun samu ‘yanci.
Babban kwamandan runduna ta bakwai ta GOC ta sojojin Najeriya Manjo Janar Waidi Shaibu ya ce ‘yan matan da aka ceto tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Yuni sun samu kulawar da ta dace kuma za a mika su ga hukumomin da suka dace nan ba da jimawa ba.
Ya ce, an kubutar da Hauwa Joseph tare da danta ne a ranar 12 ga watan Yuni 2022 a karamar hukumar Bama, yayin da Mary Dauda kuma aka kubutar da ita da danta a ranar 14 ga watan Yuni a lokacin da sojoji ke sintiri a yankin da suke da iko.
Janar Shaibu ya ce, dukkan ‘yan matan da ‘ya’yansu an yi musu cikakken duban lafiya tare da kula da su, kafin a mika su ga gwamnati wadda daga baya za ta sada su da iyayensu.
Karfin hali: ‘Yan sanda sun cafke wasu mutane 6 da ake zargin ‘yan fashin banki ne
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta cafke wasu mutane shida da ake zargin 'yan wani gungun barayin banki ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ne ya bayyana haka a garin Ibadan a ranar Litinin, inda ya ce daga cikin wadanda ake zargin akwai wani ma’aikacin kwantiragi mai shekaru 29 da haihuwa na bankin.
Rahoton jaridar Daily Sun ta ce, daya daga cikin wadanda ake zargin mace ce. Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a maboyar su da ke Agara, Unguwar Odo-Ona a Ibadan a ranar 13 ga watan Yuni bayan sun kammala shirin yin fashin wani banki a washegari.
Asali: Legit.ng